Rayuwa; me nene mararrabar Talaka da bawa a yau
idan muka yi tsinkaye muka bibiyi tarihi da kuma yadda rayuwar bayi ta kasance a shekaru da dama da suka gabata, zamu ga sun sha fama ba kaɗan ba, ta kowane fanni na rayuwa domin ana fataucin mutune kamar yadda mafarauta ke farautar dabbobin daji. Ana kama mutane daga wannan gari zuwa wancen, daga wannan kasa zuwa waccen, domin kaiwa a siyar, kuma aka dauki wannan a matsayin sana'a.
A wancen lokaci, idan ka siyo bawa a kasuwa, ya zama mamanlakinka, zaka kaishi a gidanka ne, ko gonarka koma duk inda kake bukatarsa domin yayi maka ayyukan da kake so, ko ya so ko bai so ba, wannan cilas ne a wuyansa.
To sai dai duk da haka, shi kuma mamalakin bawan ya zama wajibi a kansa cin sa da shansa kula da lafiyarsa da kuma wajan kwanansa, da tsare masa dukkanin bukatun yau da kullum.
Idan masu karatu zasu yi dogon nazari a kan wannan shimfidar zasu fahimce inda na dosa ko da kuwa ban iyar da furta abun da nake son furtawa ba.
Idan muka kalli yadda bayi a lokacin mulkin mallaka sun kayi rayuwa. Idan muka kalli yadda talakan Najeriya ke rayuwa a yau zasu dau wasu darusa masu matukar yawa.
Kamar; idan mukayi la'akari da yadda 'yan siyasa ke amfani da halsunansu wajan alkhawulla tare da yin dadin baki a duk lokacin da suke neman al'umma ido rufe, babu ko shakka abun ban tsoro ne. 'yan siyasa sun san lunguna da sakunan kauyuka da birane a lokacin yakin neman zabe, amma abunda ke ba jama'a mamaki shine yadda suke ɓacewa ɓat da zarar sun kai ga madafun iko.
A lokacin ne zasu fitar da dukkan tsare-tsaren da sun ka ga dama, wanda ya masu dadi, domin a lokacin da suka kai inda suke harare, suna sanya dukkan wani tsari wanda yayi daidai da muradunsu, ko da kuwa hakan zai jefa gwamman al'umma cikin halin ni-'ya'su.
A wannan zamani an mayar da rayuwar talaka ba a bakin komai ba, idan muka kalli yadda ake cigaba da kakabawa jama'a dokar kulle ba tare an samar masu da muhimman abubuwan da zasuyi amfani da su na yau da kullum ba, kasancewar ana tsoron kamuwa da cutar Korona mai saurin yaɗuwa, to amma kuma ba'ayi nazarin sakamakon haka mutane masu matukar yawa zasu iya kamuwa da cutar yunwa ba.
Idan muka kalli bayanin masana a sha'anin kiyon lafiya, sun tabbatar da mutum zai iya kamuwa da cutar Korona har ya warke ba tare da shi kanshi ya san ya kamu da cutar ba. To wannan kuma ya sha bamban da cutar yunwa, domin ita kan bayyana kuma ta aika mutum barzahu ba tare da bata lokaci ba.
Wani abu da ake yiwa talaka mai kama da kisan mummuke, a buge shi kuma a hanashi kuka, babu ko shakka ba za a samu cigaba ba har sai an samar da gyara.
Gyaran kuwa a dauki al'umma a matsayin bai daya, sannan shugabanni suyi adalci ga talakawa, sannan su san abun tambaya ne a kan irin jagorancin da Allah madaukakin sarki ya basu. Su kuma talakawa wajibi ne su kasance masu nuna da'a da biyayya tare da barin la'antar shugabanni, wannan kawai ce hanyar da za'a bi domin ganin an samar da al'umma managarciyya abar alfahari.
Muna fatan Allah ya sanya tausayin shugabanni ga talakawa, mu kuma Allah ya bamu ikon yi masu biyayya daidai gwargwado. A ƙarshe muna Addu'ar Allah ya bamu lafiya da zama a Najeriya Afrika da ma duniya baki daya.
Daga Nura Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment