Dokar Kulle; Jinjina ga gwamnatin Jihar Zamfara
tun bayan samun bullar cutar nan mai sarke numfashi ta Covid-19 a jihar Zamfara. A kokarin gwamna Bello Muhammad Mawatallen Maradun, na ganin ya dakile yaduwar cutar a cikin jihar tasa, yake ta shige da ficen ganin gwamman mutane basu harbu da cutara a jihar ba.
Gwamna Matawallen ya bullo da wasu sabbin tsare-tsare daga ciki har da jan hankulan al'umma wajan rage tarurukan jama'a barkatai, da kuma bayar da tazara tsakanin mutum da mutum, hadi da samar da sabulun tsaftacce hannuwa, da kuma samar da kayayyakin feshi, wanda alhamdulillahi mun sheda haka, tun lokacin da aka samar da wadannan kayan aiki, mun shedi an nada wani kwamiti mai karfin gaske, wanda ya bazama lunguna da sakuna, ma'aikatai da kuma bankuna, da unguwanni a na gudanar da aikin feshi domin kandagarkin bazuwar annobar cutar Korona mai saurin yaduwa kamar wutar daji.
Haka mun shedi irin yadda muka ga an samar da wasu mashuna masu kafa ukku, na daukar marasa lafiya, ga duk wanda aka ga ya nuna alamun kamuwa da cutar ta korona da dangoginta, hadi da wayar da kan al'umma a kan hadarin da ke tattare da wannan cuta, domin al'umma suyi taka tsan-tsan, ko shakka babu abun yabawa ne, kuma abun farin ciki ne da sambarka.
Kasancewar jihar Zamfara tana daga cikin jerin jahohin arewacin Najeriya da al'ummarta ke fama da radadin talauci. Mafi yawa daga cikin al'ummar jihar sun nuna takaicinsu a lokacin da gwamnan ya fito ya aiyana dokar takaita gudanar da sallar jam'i tare da dakatar da sallar juma'a a duk fadin jihar ta Zamfara, baya ga dokar gwamnatin tarayya wanda ta saka a duk fadin kasar na sanya dokar hana fita tun daga karfe 8 na dare zuwa 6 na asuba. Mutane da dama sun koka sosai kasancewar kaso mai yawa sai sun fito sun nema kafin zuwa a girka abinci a gida.
Mutane da dama sun nuna bacin ransu a kan wannan mataki. Gwamna Matawalle ya sanya dokar ne na takaita sallar jam'i na tsawon mako daya, sai dai wani babban abun farin ciki shine, bayan kammala makon, gwamnan ya fito yayi jawabin janye dokar hadi da yiwa al'ummar jihar gamsashen bayani akan wannan mataki da kuma dalilin daukarsa.
Ko shakka babu irin yadda gwamnan yayi saurin janje wannan doka ya sanya farin cikin a cikin zuciyoyin talakawan jihar, kasancewar kaso mai yawa daga cikin al'ummar jihar musulmai ne.
Godiya ta musamman ga gwamna Bello Muhammad Matawalle akan kokarinsa wajan ganin ya kamata adalci da gaskiya a cikin mulkinsa, muna fatan hakan zai cigaba da dorewa.
Muna kira ga sauran kafatanin gwamnonin da suka sanya dokar kulle domin takaita yaduwar cutar Korona, zasu dubi talakawansu da idon rahama su tausaya masu, in har dole ne sai dokar tayi aiki, to a fitar da tsari mai kyau da bayar da wani abu ga talakawa domin rage masu radadin abunda ke da mun su.
Fatan alheri ga gwamnatin jihar Zamfara da makarabanta masu kokarin ganin an kamanta gaskiya da adalci a tsakanin al'umma.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment