Skip to main content

Posts

Talakawa na buƙatar Tallafi

Kasancewar kowace shekara idan irin wannan lokaci ya kama, malamai hadi da dai-dai kun jama'a suna cigaba da kiraye-kiraye domin tallafawa al'umma musamman masu dankaramin karfi. To babu ko shakka, zamu iya cewa kowace shekara akwai sauki sosai idan muka kamanta ta da shakarar bana, domin kuwa ba talakawan ba har masu kudin suna jin a jikinsu, idan muna dubi yadda komai ya tsaya cik sakamakon cutar annobar korona wanda ta addabi duniya baki daya. Duk da haka, kasancewar sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, akwai bukatar masu hannu da shuni da su dubi girman Allah su taimakawa al'umma, domin ana cikin halin kuncin rayuwa, a bangarori daban-daban na sassan ƙasar nan. Babu yadda za'ayi mu samu cigaba ta kowane fanni sai in ya kasance mun sanya tausayi ga na kasa damu. Tun cen dama Najeriya tana cikin halin matsi tun kafin zuwan wannan lokaci wanda kuma mafi yawa daga cikin al'ummar ƙasar sun san haka, fatan 'yan uwanmu masu hannu da shuni, 'yan kasuwa...

ME MUKA SHIRYA DOMIN TARBON RAMADAN?

Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta shirya wani zama na musamman a ofishin kungiyar dake hannun riga da jifatu a karamar hukumar Gusau jihar Zamfara, anyi wannan zaman  ne na taron addu'o'i hadi da nasihohi domin tarbon Azumin watan Ramadan mai falala da albarka. Kafatanin shugabannin mata na wannan tafiyar ne sun ka shirya wannan zama, inda aka gayyato Malama Maryam  'Na-Inna domin ta bayar da tata gudunmuwa ga matan da suka halarci wannan zama. In da malama, tayi muhimman jawabai daga cikin harda tabo muhimmancin dake akwai wajan bayar da taimako musamman ga marayu, haka kuma ta kwadaitar da irin romon dake cikin wannan wata, a wajan Allah madaukakin Sarki. Na inna ta ce; ''Manzon Allah (S.A.W) ya yi nuni da 'yan yatsun hannayensa yace; shi da mai kula da maraya suna zo-zo-zo a cikin al'janna''. Sannan ta kara da cewar; '' tayi  murna. Da irin yadda taga wannan kungiyar mai kokarin taimakon Al'umm, babu ko shakka tayi mamak...

Matasan Ɗan Bedi sun nemi haɗin gwiwa wajan ayyukan alheri da Yazeed Trust Fund

YAZEED TRUST FUND MEDIA   A cikin kowane lokaci wannan tafiyar tana kara samun tagomashi, inda cikin ikon Allah wasu zaratan matasa da dattawa suka yi haɗin  gwiwa ga tafiyar matashin dattijo (Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani garkuwan matasan Gusau Lamidon Tsafe)  ko shakka babu a cikin kowace tafiya ana son samun mutum kamilalle irin Alh Yazeed, kasancewarsa mutum mai son ganin mutane cikin walwala da kwanciyar hankali, domin sai al'umma suna cikin walwala ne sannan zasu samu damar gudanar da lamurran yau da kullum. Idan mukayi la'akari da a kowane lokacin faɗi tashinsa shine bayar da tallafi ga masu ɗan ƙaramin karfi, a Bisa duba da irin ayukkan alherin da yake yi don ganin ya kawo ma Al'umma sauyin rayuwa, wannan ne yasa wadannan matasa sun ka ga dacewar tuntuɓa domin ganin su kansu sun bayar da kowace irin gudunmuwa a cikin wannan tafiya, ta Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani.  Matasan haɗi da dattawan,  sunyi alkawarin zasuyi wannan tafiya ba tare da jin ...

An gayyaci Yazeed Trust Fund domin kallon wasan sada zumunci

Wasan sada zumunci  da aka gayyaci Gidauniyar Yazeed Trust Fund domin  shedarwa, ya ƙayatar. A kokarin ganin an samar da dangantaka mai dorewa a tsakanin matasa a sassa daban-daba, wannan yasa kungiyaoyin wasan kallon ƙafa na Matasan gada biyu a cikin Gusau, wadannan kungiyoyin biyu sun gudanar da wasan sada zumunci domin kara karfafa dangantaka a tsakani. Wasan wanda ya gudana a jiya litinin ya kayatar sosai, a lokacin da wannan wasar ke gudana, Shugaban gidauniyar Yazeed Trust Fund (Alh, Yazeed Shehu Danfulani, garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe) wanda ke karkashin kulawar Comrd Rufa'i UB Gusau, tare da 'yan tawagarsa sun samu zuwa wajan, sun kalli yadda wannan wasa ya gudana. Comrade Rufa'a UB yace wannan gidauniya a shirye take wajan ganin ta hada ƙan waɗannan ƙungoyin wasanni na matasa a yankin, a lokacin bukukuwan sallah masu zuwa. Sannan kungiyar ta shedar da cewar, zata bayar da rigunan wasa, kyauta domin ganin an inganta wasar. A kullum babban ...

JAJANTAWA HADI DA BAYAR DA TALLAFI.

Kai tsaye daga unguwar Tsauni inda Kungiyar nan Mai son ganin jin dadi haɗi da walwalar Al'umma, musamman  masu neman taimako wato (YAZEED TRUST FUND) Karkashin Kulawar (Alh Yazeed Shehu Danfulani, Garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe). Yau ma kamar yadda ta saba yin halin nata na Alheri inda ta ziyarci Dan uwa Abokin gwagwarmaya (Saminu Gajam)  Domin jajanta masa a kan Ibtila'in gobara da ta samu gidansa Tare da bashi Tallafin kaya rage raɗaɗin wannan hali da yake ciki, sune kamar haka; Kwanon Rufi Kwaya  40 Buhun Suminti            10 Shugaban jajirtattu (Comrd Rufa'i Bala UB shi ne; ke jagorantar wannan kungiya Kuma ya hannunta Kayan ga Saminu Gajam  kamar yanda mai gayya ya bayar da umurni. WATA DABAN.... P,A na Kwamishinan Ilimi na Jihar Zamfara Babangida Bazukson ya bada nashi tallafin Bokitin Fenti 3 domin ganin ya rage wani abu daga cikin asarar da Allah ya nufa ta riskeshi. Rayyanu Mai Kaji Gusau  na K...

GIDAUNIYAR YAZEED TRUST FUND TA CIYAR DA MARAYU!

Sakamakon samun karin shekara daya daga cikin shekarun da Allah madaukakin sarki da tanadar, matashin Dattijo Alh Yazeed Shehu Danfulani Maidoya Garkuwan Matasan Gusau, kuma Lamidon Tsafe, wannan Gidauniya mai albarka ta  ciyar da Yara Marayu masara galihu a cikin Al'umm, da abinci mai gina jiki, domin kara nuna godiyarsa ga Allah madaukiakin sarki. Ko shakka babu wannan yana daga cikin godiyar Allah, idan ya maka baiwa ka gode masa, ta hanyoyin da ya tanadar abi wajan yin godiya: cikin Ikon Allah Gidauniyar Alh Yazeed shehu Danfulani, wato Yazeed Trust Fund karkashin jagorancin hadiminta, Comrade Rufa'i Bala UB salanken Galadima ta shirya gagarumin bikin ciyar da Yara marayu abinci, kyauta hadi da lemo da ruwan sha masu tsafta, domin nuna godiya akan baiwar Allah, wadda yayi masa na kara shekara daya daga cikin shekarun da Allah ya ibar masa a doron Kasa, yara marayu a sassa daban-daban sun ka samu damar halarta wannan ciyarwar, hadi da muhimman mutane da sun ka she...

ZAMU FADADA SHIRINMU NA YAZEED TRUST FUND MATERNITY CARE.......

Garkuwan matasan Gusau,Lamidon Tsafe wato Yazeed shehu Danfulani Mai Doya Gusau,ya jaddadar da ya zabi yaci gaba da zama hadimin al'umma arayuwarsa tare da bayyanar da kudurinsa akan baiwa lafiya fifiko musamman awannan lokaci da rayuwa ta soma tsada ga rayuwar bayin Allah sanadiyar cutar COVID-19. Lamidon Tsafe Yazeed Shehu Danfulani ya nuna tausayinsa ga yanda al'umma ke samun karancin shigar riba musamman Masu kananan sana'oin hannu,tare da tsaiko akan dakatuwar kasuwancinsu a wajen jahar zamfara(Yan fatauci). Hakan yasa Yazeed Danfulani yabada Umurnin fadada shirinsa na TAIMAKAWA MATA MASU DAUKE DA JUNA BIYU tare da fadakarwa akan hanyoyin kiyaye Lafiyar juna biyu da matakan dauka ayayin renon juna biyu,tare da bada Magunna Fisabilillah da fatar Allah saukar lafiya. Allah karfafa yasakama Yazeed da mafificin alhairi. YAZEED TRUST FUND. Rufai UB Gusau. 08106580400.