Yazeed Trust Fund Team A wannan talatar ne tawagar Gidauniyar (Alh. Yazeed Shehu Ɗanfulani)* ta samu shiga mareri dake shiyar Tudun Wada a nan ƙaramar hukumar mulki ta Gusau jihar Zamfara._ 31-03-2020. Inda wannan gidauniya mai albarka mai ƙoƙarin ganin ta bada tallafi ta kowace fuska, ta samu isa a makarantar malam Lawali a cikin shiyar Mareri domin bayar da tallafi ga makarantar Almajirai don rage raɗaɗin rayuwa. Ko yaushe ƙoƙarin wannan Gidauniya shi ne; taimakon marasa galihu a cikin al'umma. Haƙiƙa wannan gidauniya karkashin Jagorancin (Alh. Yazeed Shehu Ɗan Fulani Mai Doya Garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe) ta shahara matuƙa wajan ayyukan alheri ba ga ilahirin al'ummar Ƙaramar Hukumar Gusau kawai ba, a'a ayyukanta sun zarce hakan. wannan Gidauniya mai Albarka mai taken Yara masu Dara...