WANE TSARI GWAMNATIN TARAYYA DA NA JIHOHI SUN KA YIWA MASU DAN KARAMIN KARFI, BAYAN SANYAWA KASA DA JIHOHI TA KUNKUMI, DON BAYAR DA KARIYA GA CUTAR KORONA?
Duk da kasancewar cutar Karona cuta ce mai matukar hatsarin gaske, tun daga saurin yaduwa kamar wutar daji, ga kuma saurin kisa, idan mu kayi tsinkaye ga dubban al'ummar da wannan cuta ta hallaka a yankuna daban-daban na duniya, wanda hakan ya sa hatta a kasashen duniya masu karfin fada aji, da kuma karfin tattalin arziki sun girgiza sosai a sanadiyar wannan cuta.
Iya binciken masani fannin lafiya da kuma bincike mai zurfi sun tabbatar da har kawowa wannan lokaci babu ainihin takamammen maganin wannan cuta mai toshe lunfashi. Wanda haka yasa kasashen duniya suke ci gaba da garkame kan iyakokinsu, domin takaita illar cutar.
Kasashe daban-daban na duniya suna fitar da wani tallafi na musamman domin bayarwa ga ilahirin al'ummarsu, wanda hakan zai rage masu radadin halin matsi da suke ciki, sakamakon killacesu da akayi a gida, har zuwa lokacin da gwamnatocin kasashen sun ka kaiyade fara zarga-zarga.
Tuni ita ma Najeriya na shiga cikin jerin gwanon gwamnatocin duniya wajen rufe kan iyakokinta, don kandagarkin cutar coronavirus mai saurin yaduwa. Hakan ya samo asali ne, saboda ganin irin yadda wannan kwayar cuta ke ci gaba da ruruwa a cikin kasar ta Najeriya.
Ko shakka babu mun yaba matuka ainun ga gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari hadi da ilahirin jerin gwanon gwamnoni baki daya akan irin matakan da sun ka dauka, na killace kasa, dama sassan kasar baki daya domin ta kaita wannan annoba.
Saura da mi, bayan cutar Korona, akwai wata cuta ta yunwa. Na tabbata kashi 80 cikin 100 na mutanen Najeriya Talakawa ne, wasu daga cikinsu suna cikin halin tsadar rayuwa, domin wasu sai sun fito sun nema sannan su koma su baiwa iyalansu.
Shin gwamnatin Najeriya wane tsari tayi ga irin wadannan bayin Allah? Kamar yadda mun ka sha gani a sauran wasu kasahe, inda ake bi ana tallafawa al'umma da kayan abinci. Yana da kyau gwamnatin tarayya ta fito da irin wannan tsarin domin rage radadin talaucin da yayi wa al'umma daurin gwarmai!
Haka jihohin da su kansu suka dauki matakin rufe iyakokin jihohinsu domin hanawa da yada cutar covid19, ko wane tsari sun ka yiwa al'ummarsu, wanda zai taimakawa jama'a kafin adadin tsawun makwannin da za a kwashe kafin bude kan iyakokin da zasu kasance a garkame?
Idan har an samar da wani tallafi ga bayin Allah marasa galihu, to lallai a tsaya ayi tsari mai kyau wanda tallafin zai kai ga wadanda aka bayar da tallafin dominsu, don kaucewa babba da jika!
Muna fatan Allah ya ta kaita wannan cuta, yayi mana maganinta. Wadanda sunka kamu Allah ya basu lafiya, wadanda basu kamu ba, Alah ya kare su da kamawa da wannan cuta mai tayar da hankali.
Daga Nura Mai Apple
Comments
Post a Comment