KUNGIYAR STUDENT ALLIANCE SUPPORT OF BELLO MUHAMMAD MATAWALLE (SA-BELMAT)
KUNGIYAR STUDENT
tayi zama yau daya daga cikin wadanda suka kirkiro da wannan kungiya wato Comrade Umar Mahmud Umar, ya ce; "babban makasudin zaman shine munga ya dace mu fito a matsayinmu na 'yan jiha, kuma a matsayinmu na wani yanki daga cikin daliban jihar Zamfara muyi godiya ta musamman bisa ga irin gwaggwarmaya da chanji da Hon Luqman Majidadi ya kawo karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Zamfara na bashi wannan jagorancin, da kuma shi gwamna a bisa babban aikin da ya dauko wajan ganin a samu ilimi a cikin jihar Zamfara".
Ya ce; "kamar yadda muka sani akwai dalibai wajan 700 daga jihar zamfara wadanda aka dauko kuma aka tantance mutum 200 daga ciki zasu je suyi karatun a bangare daban-daban tun daga abinda ya shafi bangare tiyata da kuma hada magunguna da sauransu, wanda insha Allahu nan da shekaru zuwa goma zamu samu 'yan asalin jihar Zamafar da suka samu kwarewar da zasu ci gaba da kula da 'yan uwansu a cikin kauyuka da kuma biranen jihar Zamfara, wanda in aka dubi tun inda aka fito shekara goma ba'a taba samun gwamnatin da tazo cikin lokaci daya ta daukin nauyin dalibai sama da 200 ba, ko kuma wani abu mai kama da haka, sai a karkashin jagorancin wannan gwamna, to shi yasa muka ga ya kamata muzo mu bayyanawa duniya jin dadinmu a bisa irin wannan namijin kokari da ake yi".
Yace; "kamar yadda kuke gani irin namijin kokarin da shugaban daliban jihar Zamfara wato (Hon, Kuqman majidadi keyi, tun daga wajan tantance dalibai, hadi da samar masu da tikiti da kula dasu da samar masu da muhali mai kyau a kasashen ketare abun yabawa ne". Yace; zuwan Majidadin, ke da wuya a ofis ya dukufa wajan ziyarce-ziyarce a wasu manyan jami'o'in kasar nan, domin yin bincike akan shin wane bashi ne waccan tsohuwar gwamnati ta bari wanda su yanzu zasu dubi kokarin da ya kamata suyi, saboda akwai daliban jihar Zamfara masu karatu Al'hikima har yanzu basu karbi dakardunsu ba, akwai wasu an kaisu sunyi karatu a kasar India biyan kudin ya gagara, to wannan ba karamin kokarin bane" a cewar Comrade Umar.
Haka ya kara da cewar "kungiyar (Sa-Belmat) tun lokacin da aka kirkireta ta samar da ayyukanyi ga matasa". A karshe yayi godiya ga gwamna Bello Muhammad Matawalle akan rakiyar da yayi wajan ganin cewa an wayar da kan jama'a kan cin hanci da rashawa. Haka yayi addu'ar samun zaman lafiya da arziki mai albarka a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
Sharhi;
munyi jinjina sosai da wannan kungiya idan maka dubi irin kokarinta wajan samar da cigaba ga matasa, muna fatan gwamnatin gwamna Bello Muhammad Matawalle zata kara kaini domin ganin matasan jihar Zamfara sun samu ilimi mai nagarta wanda zai taimaki jihar nan ta kowane bangare
Daga Nura Muhamad Mai Apple Gusau

Allah kara temakama gwamna
ReplyDeleteAllah kara temakama gwamna
ReplyDelete