Zuwa ga mai girma Gwamnan Jihar Zamfara



Assalamu alaikum.

Bayan sallama irin ta addinin musulunci, cike da girmama a matsayina na talakanka, kuma wanda yake a karkashin jagorancinka a wannan jiha tamu mai albarka wanda bamu da wata jiha bayanta. Nake bayyana ra'ayi na, a bisa wannan nazari naka na ganin jihar Zamfara ta kece tsara a sauran jihohin da muke da su a cikin kasar nan na gina sabon gidan gwamnati la'akari da irin yadda aka barmu a baya ta gefen babban gida, mallakar gwamnati. Babu ko shakka wannan nazari ne mai kyau kuma abun so ne, kuma ci gaba ne mai alfanu, Allah ta'ala ya mana jagora, Amin!

Ba zan so na kaucewa daftarin tsarin dokar kasar nan ba, na damar da aka bawa 'yan kasa na fadin albarkacin baki, cikin sashe na 39 karamin sashe na kundin tsarin mulkin kasar nan. A kowane lokaci irinmu masu nazari da sharhi akan al'amurran yau da kullum ba'a rasa mu da tsegumi akan wasu abubuwa mabambanta akan abunda suka shafi kasar nan dama wasu jihohi wani lokacin ma har da wasu kasashen ketare.

Ranka ya Dade Sir! Hakika akwai wasu muhimman abubuwa da sun ka fi wannan aiki muhimmanci. Hakika aniyar Gwamnatinka na gina sabon katafaren gidan gwamnati wanda zai lakume zunzurutun kudi har Naira miliyan dubu bakwa 7 a wannan shekara ta 2020. Wani babban kuskure ne idan muka dubi irin yadda jihar bata gama tasowa ba daga cikin babban ƙalubalen da ta fuskanto cikin shekarun baya, tabbas waɗannan kuɗaɗe sunyi matukar yawa, kasancewer yanzu haka akwai wasu sassa a cikin jihar inda basu  da wadatattun ruwan sha, hadi wuraran shan magani, ballantana uwa uba wutar lantarki.


 A duk cikin kasar nan Zamfara ce kawai Jihar da bata da jami'a mallakar gwamnatin jiha. Mafi yawa daga cikin 'ya'yan talakawa basu iya karatu a jami'ar gwamnatin tarayya da muke da ita a cikin jihar nan. saboda rashin abin yi kuma ana bukatar karatun, zai kyautu matuka a fifita ta koma bayan wannan aiki, a nawa Nazarin!

Tun kafin aje ko ina a cikin babban birnin jihar wato Gusau har yanzu ba'a samu wadatattun ruwan sha ba, to ballantana ayi maganar wasu ƙananan hukumomi da sauran gundumomi zuwa ƙauyuka. Lallai ne mai girma gwamnan jihar Zamfara a sake dubawa haɗi da nazari akan wannan lamari, domin kana da matuƙar ƙima da kwarjini a idanun mutanan jihar Zamfara musamman talakawa.

Mun san cewa shi gyara abun so ne, to amma adadin kudin da wannan aiki zai ci zai bar wani wagegen giɓi a kasafin kuɗin wannan shekarar ta 2020, tattalin arziƙin jihar Zamfara baida ƙarfin da za'a iya fitar da waɗanannan ƙuɗaɗe ba tare da ya girgiza ba, idan mukayi  la'akari da jihar Zamfara bata da wasu manyan hanyoyin da kuɗaɗen shiga ke zuwa, kamar sauran wasu jihohi, irin Jihar Kano da Jihar legas, da wasu manyan jihohin ƙasar nan, muna roƙon mai girma gwamna a matsayinsa na mai kishin talaka yayi nazari mai zurfi a bisa wannan yunƙuri.


Wasu daga cikin ƙananan asibitocinmu suna matuƙar buƙatar muhimmiyar kulawa, musamman yadda za'a kawo marar lafiya, amma babu isassun jami'an kiyon lafiya. Sannan hanyoyin ƙarkara sunyi matuƙar lalacewa musamman idan yanayin damina ya zo. Wasu hanyoyi ba a iya biyarsu duk da tarin kasuwannin da ke cikinsu.

Haka fannin samar da ruwan sha wadatattu yankunan karkara suna da matuƙar buƙatar hakan suna buƙatar samar da fanfunan tuƙa-tuƙa ko manyan riyojin murtsatse, muna roƙo gareka mai girma gwamna! ya kamata hankalinka ya karkato a wannan fanni, domin ganin jihar ta samu ci gaba ta kowane fani hadi da mutanenta sun amfana da romon mulkin demokaradiyya. Allah ya baka ikon ganin wannan ra'ayi nawa, domin a dubi talaka da idon rahama. Fatan alheri ga reka, Allah ya ci gaba da yi maka jagora a cikin mulkinka.

 Nura Muhammad

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’