Yazeed Trust Fund Team
A wannan talatar ne tawagar Gidauniyar (Alh. Yazeed Shehu Ɗanfulani)* ta samu shiga mareri dake shiyar Tudun Wada a nan ƙaramar hukumar mulki ta Gusau jihar Zamfara._
31-03-2020.
Inda wannan gidauniya mai albarka mai ƙoƙarin ganin ta bada tallafi ta kowace fuska, ta samu isa a makarantar malam Lawali a cikin shiyar Mareri domin bayar da tallafi ga makarantar Almajirai don rage raɗaɗin rayuwa. Ko yaushe ƙoƙarin wannan Gidauniya shi ne; taimakon marasa galihu a cikin al'umma.
Haƙiƙa wannan gidauniya karkashin Jagorancin (Alh. Yazeed Shehu Ɗan Fulani Mai Doya Garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe) ta shahara matuƙa wajan ayyukan alheri ba ga ilahirin al'ummar Ƙaramar Hukumar Gusau kawai ba, a'a ayyukanta sun zarce hakan.
wannan Gidauniya mai Albarka mai taken Yara masu Daraja. ta Yazeed Trust Fund, ƙarƙashin ƙulawar (Comrade Rufa'i Bala U&B Salanken Galadima) ta kaiwa makarantar Almajirai masu daraja tallafin Abinci mai rai da lafiya wanda ko ina ana iya cinsa, domin karawa jiki garkuwa, Almajiran sun yi murna sosai da wannan tallafin abinci da suka samu daga wannan bawan Allah. A ƙarshe sunyi addu'ar Allah ya saka masa da mafificin alheri. Haka shima malamin wannan makaranta ya godewa wannan gidauniya da wannan tawaga sannan yayi addu'ar fatan alheri.
Alheri bashi da ƙadan, Mutane nason masu kyautata masu, Allah ma yana son masu kyautata wa mutane.
Nura Mai Apple.
Comments
Post a Comment