Coronavirus; Me kuke so ku sani kan matakan kariya daga cutar Covid19




Wadan ne abubuwa ne kuke so ku sani, sannan wadanne matakan kariya kuke so ku sani kan wannan cuta 
Ya  gwamnatin Najeriya ta hana mutane baki shiga da fita a kasar nan sannan gwamnati ta fara gudanar da bincike domin gano ko akwai mutanen da suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da dan kasar Italy a jihohin Legas da Ondo.
Daga nan hukumar hana yaduwar cututtuka ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar da hukumar ta bada.
HANYOYIN SAMUN KARIYA DAGA CUTAR:
1. Yawaita wanke hannu da ruwa da sabullu ko kuma da man tsaftace hannu ‘Hand Sanitizer’ idan babu ruwa.
2. A rika tsaftace muhalli.
3. Idan za a yi tari ko kuma atishawa a yi amfani da tsumma domin kare baki da hanci.
4. A guji yawan kusantan mai fama da mura ko kuma alamomin cutar.
5. Wurarren aiki su tabbatar sun ajiye ruwa da sabullu domin ma’aikata su rika wannke hannu ko kuma a ajiye man tsaftace hannu.
6. A guji shan magani ba tare da izinin likita ba.
7. Gaggauta zuwa asibiti na cikin hanyoyin da zai taimaka wajen warkar da cutar a jikin mutu.
8. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun kare kansu yayin da suke gudanar da aiyukkansu.
9. Za a iya kiran wannan lambar 07032864444 a duk lokacin da ba a ji daidai ba a jiki.

Comments

  1. Allah ya kare musulmi baki d'aya, da kamuwa da wannan mugunyar cutar.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’