GALADIMA WARD SOCIAL MEDIA TEAM.

GALADIMA WARD SOCIAL MEDIA TEAM.


A  yau lahadi 15/03/2020 wannan kungiya ta fara zamanta na farko, kan abinda ya shafi matsalolin yankin da suke ciwa mutanen yankin tuwo a kwaryar , duba da yadda a duk cikin jihar Zamfara musamman a Gusau babu wata gunduma da tafi Galadina girma da kuma yawan al'umma. Wannan ne babban abun da ya ji hankalin matasan yankin wajan ganin sun assasa wannan kungiya da zimmar kawo kyakkyawan sauyi a cikin shiyar ta galadima.

Shiyar galadima shiya ce wadda Allah ya albarka da hazikin matasa masu kokarin ganin an samu sauye-sauye mai ma'ana a kowane bangare a jihar Zamfara ba kawai yankin ba.

Wannan zama ya gudana ne a shiyar hayin dan hausa, dake sabon fege a yankin na galadima. Zaman ya samu halartar dinbin matasa a sassa daban-daban na yankin, sannan an tattauna muhimman batutuwan da za su kawo cigaba a cikin wannan tafiyar.

Saboda haka muna cike da fata da burin ganin wannan tafiya an samu nasararta wajan ciyar da yankin a gaba


Tahoto Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Copyright@nuramaiapple



Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’