Bikin Gidauniyar Yazeed Dan Fulani ya Ƙayatar
A jiya ne gidauniyar Alh, Yazeed Shehu Dan Fulani Mai Doya tayi gagarumin bikinta, bikin yana zuwa ne a daidai farko-farkon wannan sabuwar shekarar ta miladiyya, bikin wanda ya gudana jiya Asabar 4 ga watan Junairun wannan sabuwar shekarar ta 2020.
Manufar dai wannan bikin shine bayar da tallafi na musamman ga wasu
jajirtattun 'yan kasuwa daban-daban a jihar nan waɗanda sunka sadaukar da lokacinsu wajan ganin jihar Zamfara ta samu haɓaka a fannin tattalin arziƙi, anyi nazarin wannan shirin ne domin ƙara wa 'yan kasuwar Jihar Zamfara kwarin gwiwar ci gaba da bada tasu gudunmuwa ta fuskoki da dama.
Ɗan Fulanin ya jagoranci bayar da wasu kyaututuka na lambar yabo, watau lambar girmamawa ga mutanen da sun kayi zarra a fagen kasuwa. Kyautar ta lambar ban girma tazo ne a matakai daban-daban. Idan dai ba'a manta ba, ko za'a iya tunawa kafin zuwa ranar bikin an gudanar da wani zaɓe a kafar sadarwar yanar gizo, wanda Yazeed Trust Fund ta shirya kuma ta gabatar, wanda hakan ya ba da cikakkiyar nasara ga waɗanda sunka yi nasarar cin gasar.
A lokacin da bikin ke gudana wasu daga cikin 'yan wasar barkwanci sun nishaɗantar da al'umma. Bikin wanda ya samu halartar manyan baki a sassa daban-daban a ciki da wajan jihar ta Zamfara, anyi bikin kuma an kammala cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankala.
Rahoto daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.
Comments
Post a Comment