Skip to main content

Posts

Zuwa ga mai girma Gwamnan Jihar Zamfara

Assalamu alaikum. Bayan sallama irin ta addinin musulunci, cike da girmama a matsayina na talakanka, kuma wanda yake a karkashin jagorancinka a wannan jiha tamu mai albarka wanda bamu da wata jiha bayanta. Nake bayyana ra'ayi na, a bisa wannan nazari naka na ganin jihar Zamfara ta kece tsara a sauran jihohin da muke da su a cikin kasar nan na gina sabon gidan gwamnati la'akari da irin yadda aka barmu a baya ta gefen babban gida, mallakar gwamnati. Babu ko shakka wannan nazari ne mai kyau kuma abun so ne, kuma ci gaba ne mai alfanu, Allah ta'ala ya mana jagora, Amin! Ba zan so na kaucewa daftarin tsarin dokar kasar nan ba, na damar da aka bawa 'yan kasa na fadin albarkacin baki, cikin sashe na 39 karamin sashe na kundin tsarin mulkin kasar nan. A kowane lokaci irinmu masu nazari da sharhi akan al'amurran yau da kullum ba'a rasa mu da tsegumi akan wasu abubuwa mabambanta akan abunda suka shafi kasar nan dama wasu jihohi wani lokacin ma har da wasu kasashen...

Bikin Gidauniyar Yazeed Dan Fulani ya Ƙayatar

A jiya ne gidauniyar Alh, Yazeed Shehu Dan Fulani Mai Doya tayi gagarumin bikinta, bikin yana zuwa ne a daidai farko-farkon wannan sabuwar shekarar ta miladiyya, bikin wanda ya gudana jiya Asabar 4 ga watan Junairun wannan sabuwar shekarar ta 2020. Manufar dai wannan bikin shine bayar da tallafi na musamman ga wasu jajirtattun 'yan kasuwa daban-daban a jihar nan waɗanda sunka sadaukar da lokacinsu wajan ganin jihar Zamfara ta samu haɓaka a fannin tattalin arziƙi, anyi nazarin wannan shirin ne domin ƙara wa 'yan kasuwar Jihar Zamfara kwarin gwiwar ci gaba da bada tasu gudunmuwa ta fuskoki da dama. Ɗan Fulanin ya jagoranci bayar da  wasu kyaututuka na lambar yabo, watau lambar girmamawa ga  mutanen da sun kayi zarra a fagen kasuwa. Kyautar ta lambar ban girma tazo ne a matakai daban-daban. Idan dai ba'a manta ba, ko za'a iya tunawa kafin zuwa ranar bikin an gudanar da wani zaɓe a kafar sadarwar yanar gizo, wanda Yazeed Trust Fund ta shirya kuma ta gabatar,...

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

KALAMAN GWAMNA BELLO MUHAMMAD MATAWALLE NA JIHAR ZAMFARA A KAN TSOHON GWAMNA AA YARI

a falsafa irin ta siyasa wanda muke gani tana gudana a daidai wannan lokaci, bayyane take karara kalaman gwamnan jihar Zamfara (Rt,Hon Bello Muhammad Matawallen Maradun) jan kunne ne ga tsohon gwamnan jihar Zamfara (Dr, Hon Abdul-aziz Abubakar Yari shattiman Zamfara) kuma jan kunne ne ga dukkanin wani mai kokarin yin tugu ga zaman lafiyar da ake ganin jihar ta samu tun bayan kame madafun ikon da shi wannan gwamna Bello Matawalle yayi. Idan muka yi dubi a mahanga irin ta siyasa zamu ga cewa mutum zai iya yin duk wani abu domin cimma wata manufa ko da kuwa hakan zai iya bakanta ran dubban al'umma, faifan bidiyon da ya bayyana a ranar Alhamis 21 ga watan Satumbar 2019 ya ja hankulan dubban mutane a sassa daban-daban na kasar nan da wasu kasashen ketare, inda an ka gano gwamnan Bello Matawalle shi da kansa ya na bayyana irin ƙwaƙwaran matakin da zai dauka ga tsohon gwamnan AA Yari. Idan dai zamu iya tunawa gwamnan ya sha kiran taron 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC a gid...

Gidauniyar Yazeed Danfulani ta dau nauyin karatun yara 20

* YAZEED DANFULANI TRUTS FUND * _wannan foundation mai suna a sama karkashin kulawar * (Alh. Yazeed Shehu Dan Fulani) * ya ziyarci fadar masarautar Mayana a gundumar Mayana a karamar hukumar mulkin Gusau a jihar Zamfara, domin neman tubarrakin masarautar, hadi da bayyana dukkanin kuduroran wannan kungiya wajen bada muhimmiyar gudunmuwa a bangaren ilimi. _A lokacin ziyarar an tattauna muhimman jawabai akan kudurin ganin yara masu tasowa sun samu nagartacciyar tarbiyya, da kuma tasowa da kyakkyawar mu'amala a cikin al'umma, kasancewar yaro na kowa ne!_ _Bayan nan an gabatar da yara Kanana Mata da Maza har su Ashirin 20 wadanda an ka dinkawa uniform hadi da basu kayan karatu kyauta da daukar nauyin karatunsu a matakin Primary a cikin gundumar ta mayana._ _Ilimi shine ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a duniya! A dalilin haka yasa wannan * Foundation * ya himmatu wajen ganin yara sun samu ilimi don tallafawa kansu da al'umma._ _Masar...

Najeriya Barka da samun 'yancin kai shekara59

Najeriya Kasa mai albarka, hakika muna godiya ga Allah ta'ala da ya nuna mana Najeriya ta cika shekara 59 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniyya, duk wani dan kasa na gari ya zama wajibi yayi murna da wannan rana, domin abun alfahari ce ga 'yan Najeriya kwata. Ya zama wajibi muyi jinjina ga 'yan mazan jiya, wato  Sir Ahmadu Bello Sardaunan sakkwato. Da Sir Abubakar Tafawa ɓalewa, da sauran wadanda lokaci ba zai bani damar zaiyana su ba,  wadannan jajirtattun mutane sun taka muhimmiyyar raya wajen hada kan kasar nan domin kasancewa turba daya, kuma a matsayin tsintsiya madauri daya. Muna addu'ar Allah yayi masu sakayya da gidan al'janna. A bisa wannan ya kamata shuwagabannin wannan zamani suyi kwaikwayon kyakkwan halayen wadannan bayin Allah domin ganin kasar nan ta ci gaba da zama a matsayin turba daya, idan har ana son ganin kasar nan ta cigaba da zama a matsayin abu daya, to lallai ne shuwagabannin kasar su sanya kishin kasa gaba ...

Makomar Najeriya a kasashen duniya a taron koli na majalisar dinkin duniya

KO NAJERIYA TA TABA SAMUN WANI ALFANU A CIKIN TARON DA TAKE HALLARTA A ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA?                Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Kamar yadda ake ci gaba da gudanar da ire-iren wadannan tarurruka a shekara-shekara wanda wannan shine 74 a cikin jerin tattaunawar da ake a zauren majalisar dinkin duniya. Najariya Kasa ce Mai albarka kuma tana da kima da daraja a idon duniya Wanda hakan ya sa itama tana daya daga cikin manyan baki masu jawabi a cikin zauren na majalisar. Taron Wanda yake gudana, kuma manufar taron na bana shine kalubale na sauyin yanayi, Wanda ake kokarin ganin an tallafawa kasashen duniya masu fama da wannan matsalar, kuma a cikin taron har wasu gwamnatocin kasashen duniya sun Fara bayar da tallafinsu a cikin wannan shirin, shirin Wanda ya samu bakuntar kasashe 66 a bana.                 Shugaban majalisar dinkin duniya Antonio kutaresh Manyan kasashen da ...