Gidauniyar Yazeed Danfulani ta dau nauyin karatun yara 20
*YAZEED DANFULANI TRUTS FUND*
_wannan foundation mai suna a sama karkashin kulawar *(Alh. Yazeed Shehu Dan Fulani)* ya ziyarci fadar masarautar Mayana a gundumar Mayana a karamar hukumar mulkin Gusau a jihar Zamfara, domin neman tubarrakin masarautar, hadi da bayyana dukkanin kuduroran wannan kungiya wajen bada muhimmiyar gudunmuwa a bangaren ilimi.
_A lokacin ziyarar an tattauna muhimman jawabai akan kudurin ganin yara masu tasowa sun samu nagartacciyar tarbiyya, da kuma tasowa da kyakkyawar mu'amala a cikin al'umma, kasancewar yaro na kowa ne!_
_Bayan nan an gabatar da yara Kanana Mata da Maza har su Ashirin 20 wadanda an ka dinkawa uniform hadi da basu kayan karatu kyauta da daukar nauyin karatunsu a matakin Primary a cikin gundumar ta mayana._
_Ilimi shine ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a duniya! A dalilin haka yasa wannan *Foundation* ya himmatu wajen ganin yara sun samu ilimi don tallafawa kansu da al'umma._
_Masarautar tayi jinjina ga wannan kungiya hadi da addu'ar Allah ya sakawa wannan bawan Allah da mafificin alheri, haka masarautar tayi kira ga sauran ɗaiɗaikun jama'a da ma kungiyoyi da suyi koyi da wannan kungiyar wajen tallafawa gajiyayyu da marayu da marasa gata a cikin al'umma._
_Bayan kungiyar ta kammala baje kolin abun alherin a gaban masarautar, ta zarce *makarantar Birnin Ruwa Primary School* domin tasa keyar yaran da sun ka amfana da wannan tallafi a gaba don hannintasu ga shugaban makarantar ta birnin ruwa. *Yazeed Trust Fund* tayi kicibus da shugaban makarantar in da shima ya bayyana farin cikinsa a kan wannan kokari, inda yace tun lokacin da ya fara koyarwa a makaranta a shekara 1999 har zuwa wannan lokaci bai taba ganin wata kungiyar da tayi irin wannan nazarin ba, shugaban kungiyar Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala U&B yace wannan kungiya a shirye take ka'in-da-na'in wajan bada tallafi iya karfinsu domin ganin al'umma sun cigaba. Rufa'i Bala U&B yana tare da rakiyar wasu daga cikin shuwagabannin kungiyar da sauran Exco da membobin kungiyar a wajan yin wannan muhimmin aikin alheri._
_Idan dai za a iya tunawa ko ba a manta ba wannan Foundation ya lashi takobin shiga lunguna da suƙunan wannan karamar hukuma domin bada taimako daidai gwargwadon hali. Ko yaushe taken tafiyar dai shine tallafawa yara masu darajja, da wannan muke rokon Allah ta'ala ya sanya albarka da alheri ga wadannan yara yayi wa rayuwarsu albarka._
*Fatan Alheri ga Yazeed Trust Fund*
_*Daga Nura Mai Apple Reporter Media News*_
Copyright@nuramaiapple
Comments
Post a Comment