Najeriya Barka da samun 'yancin kai shekara59



Najeriya Kasa mai albarka, hakika muna godiya ga Allah ta'ala da ya nuna mana Najeriya ta cika shekara 59 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniyya, duk wani dan kasa na gari ya zama wajibi yayi murna da wannan rana, domin abun alfahari ce ga 'yan Najeriya kwata.

Ya zama wajibi muyi jinjina ga 'yan mazan jiya, wato  Sir Ahmadu Bello Sardaunan sakkwato. Da Sir Abubakar Tafawa ɓalewa, da sauran wadanda lokaci ba zai bani damar zaiyana su ba,  wadannan jajirtattun mutane sun taka muhimmiyyar raya wajen hada kan kasar nan domin kasancewa turba daya, kuma a matsayin tsintsiya madauri daya. Muna addu'ar Allah yayi masu sakayya da gidan al'janna.

A bisa wannan ya kamata shuwagabannin wannan zamani suyi kwaikwayon kyakkwan halayen wadannan bayin Allah domin ganin kasar nan ta ci gaba da zama a matsayin turba daya, idan har ana son ganin kasar nan ta cigaba da zama a matsayin abu daya, to lallai ne shuwagabannin kasar su sanya kishin kasa gaba koma bayan bukatun kansu dana 'yan uwansu.

Kowane dan Ƙasa yana da irin rawar zai iya takawa wajan ciyar da kasar a gaba, ta hanyar bayar da hadin kai, ta fuskar zaman lafiya da hadin kan juna, da nuna da'a da halin dattako a duk inda ya tsintsi kansa.

Najeriya kasa ce mai matukar ƙima da kwarjini a idanun duniya, to idan muna son kasar nan ta cigaba da kasancewa a haka, to sai mun tsayu haikan gaskiya da gaskiya, mun yi aiki tare hadi da son juna, don kasar ta cigaba da rike kambunta.

Sai malamai na addinai daban-daban da muke da su a cikin kasar nan sun himmatu wajen kiraye-kiraye ga mabiyansu, su nuna musu hanyar gaskiya hadi da sanar da su tsantsar gaskiya, domin samun hadin kan kasa ta hakan ne arzikin kasar nan zai samu bunkasa, kasancewar Allah yayi wa 'yan Najeriya hikima da fasaha da sanin dabaru daban-daban, muna fatan Allah ya cigaba da saukar da albarka a cikin Najeriya.

Mutanen da Allah ya dorawa alhakin kula da talakawa wato shugabanninmu ya kamata su kara tanke damarar tallafa wa 'yan ƙasa don inganta rayuwarsu domin ganin an tafi da kowa bai daya.


Ina amfani da wannan damar domin fatan alheri ga Shugaban Kasar Najeriya Muhammdu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da dukkanin gwamnonin Najeriya baki daya.

Allah ya karo albarka ga kasa ta Najeriya da arziki mayilwaci.

Muna murna da samun yancin Kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniyya !

Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau 08133376020

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’