Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba.
Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala.
Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana. 
Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare? 
Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi fahimtar. Ba lallai ba ne hange na  ya zo ɗaya da na ka. Ba lallai ba ne kowa yayi imani da abin da na yi imani da shi. Yadda kake ji da addininka haka wani ma haka yake ji da nasa amma don ra’ayinmu ya sha bamban ta wani gefe ba lallai ba ne a samu bambanci ta ko’ina. Akwai yiwuwar samun daidaito a wani fanni na rayuwa.
Ba zan manta ba a lokacin da na je daukan rahoton zanga-zangar bijirewa kudirin haramtawa Musulmi shiga Amurka, da dama daga cikin wadanda suka fito kwansu da kwarkwatarsu don marawa Musulmi baya  ‘yan luwadi ne, duk da cewa sun san matakin Musulunci har ma da addinin Kirista a kan irin tsarin rayuwarsu. Da na nemi sanin dalilin fitowarsu, sai daya daga cikinsu ya ce ya fito ne saboda ya san zafin tsangwama da wariya saboda haka ba zai amince ya ga ana yi wa wani haka ba tare da ya yi wani abu ba. 
Wannan ya bude min ido sosai, ko da ban amince da salon rayuwarsa ba, akwai wani abun karin ilmi da na koya. Ya nuna min cewa za ka iya jingine bambanci ko kyama domin a yi aiki tare kan wani abu muhimmi da ya shafi kowa.
Don haka babu ruwana da girman kai wajen neman ilimi kuma babu ruwana da wata gardama don na san ba zan iya sauya wa kowa ra’ayi ba. 
Kowa ka hadu da shi, ka dauke shi a matsayin wata dama na karin ilimi don watakila akwai wani abun da ya sani wanda kai ba ka san shi ba ko kuma a cikin musanyar ra'ayin ku, ka tsinci abin da bature ke cewa *“an aha moment”* wato karin haske kan wani ilimi na rayuwa. 
Idan ka jingine na ka tunanin ka saurari ra’ayin da ya sha bamban da naka za ka ga koda ba ka amince da ra’ayin ba, za ka samu fahimtar dalilin da ya sa wannan mutumin ke da wannan ra’ayin. Hakan shi ma, karin ilimi ne. 
A wannan zamani da muke fama da matsalolin da babu iyaka dole sai mun ajiye bambance-bambancen da muke da su, mun hada kai domin mu gudu tare mu tsira tare. 
Don haka jama’a mu saurara fiye da yadda muke magana domin mu fahimci juna.

Comments

Popular posts from this blog

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’