KALAMAN GWAMNA BELLO MUHAMMAD MATAWALLE NA JIHAR ZAMFARA A KAN TSOHON GWAMNA AA YARI
a falsafa irin ta siyasa wanda muke gani tana gudana a daidai wannan lokaci, bayyane take karara kalaman gwamnan jihar Zamfara (Rt,Hon Bello Muhammad Matawallen Maradun) jan kunne ne ga tsohon gwamnan jihar Zamfara (Dr, Hon Abdul-aziz Abubakar Yari shattiman Zamfara) kuma jan kunne ne ga dukkanin wani mai kokarin yin tugu ga zaman lafiyar da ake ganin jihar ta samu tun bayan kame madafun ikon da shi wannan gwamna Bello Matawalle yayi.
Idan muka yi dubi a mahanga irin ta siyasa zamu ga cewa mutum zai iya yin duk wani abu domin cimma wata manufa ko da kuwa hakan zai iya bakanta ran dubban al'umma, faifan bidiyon da ya bayyana a ranar Alhamis 21 ga watan Satumbar 2019 ya ja hankulan dubban mutane a sassa daban-daban na kasar nan da wasu kasashen ketare, inda an ka gano gwamnan Bello Matawalle shi da kansa ya na bayyana irin ƙwaƙwaran matakin da zai dauka ga tsohon gwamnan AA Yari.
Idan dai zamu iya tunawa gwamnan ya sha kiran taron 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC a gidansa dake Talatar Mafara domin tattaunawa akan abubuwa mabambanta, wanda hakan yakan kara tunzura magoya bayansa da yin wasu batutuwa na daban. Babu ko shakka sha'ani irin na tsaro bai kamata a siyasantar da shi ba, domin idan har abinda gwamnan jihar Zamfara yake hasashe ya tabbata gaskiya, babu shakka wannn ya kasance kamar cin amanar kasa ne.
Tsarin zaman lafiya abu ne wanda duk a duniya babu wata kasa da ba ta yin na'am da shi, kuma babu wata kasa a duniya da zata lamunci safgar ta'addanci domin babban laifi ne, kuma cin amanar kasa ne, to uwa-uba a Najeriya wanda zaman lafiyar ta yake tangal-tangal, musamman a Arewa wanda tafi fuskantar kalubale a sha'anin tsaro da sauran abubuwa na daban. Duk dan Jihar Zamfara wanda Da ya san inda aka fito, baya marhabun da duk wani tsari wanda zai shafi tada zaune tsaye.
Neman Zaman lafiya........
muna kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Zamfara da duk wani mai alhakin samar da tsaro a jihar Zamfara da cewa lallai ne ayi duk mai yiwuwa domin kara zage damtse wajan ganin zaman lafiya ya samu gindin zama a jihar nan. A na siyasantar da komai amma ban da sha'anin tsaro, domin rayukan al'umma ba wasa bane, kuma sai da al`ummar ne sannan kowane irin shugaba zai iya gudanar da mulkinsa.
Lallai kowane shugaba ya sanya tsoron Allah a cikin al'amurransa domin ganin jihar nan ta kai ga tudunmun tsira. Sa ido kan sha'anin mulki nauyi ne wanda ya rataya a wuyan masu shugabantar al'umma a matakai daban-daban, kuma inkiya, ko hannunka mai sanda yana da muhimmancin gaske a sha'anin a shugabanci.
Muna bada shawara ga al'ummar jihar Zamfara a kan muhimmancin zaman lafiya a cikin al'umma. Duk wata ƙasa da ta samu haɓaka da ci gaba a duniya, ci gaban bai samu ba sai da zaman lafiya. Su kansu waɗanda ake amfani da su wajan tayar da ƙayar baya, ana amfani da su ne kawai domin cimma wata manufa wanda kuma hakan babban kuskure ne kuma cin amanar ƙasa ne.
Babu ko shakka kalaman gwamnan a daidai wannan gaɓar yayi a lokacin da ya dace, domin shi icce tun yana danye ake lankwasashi.
Mafita ......
Riga kafin wannan babban kalubale shi ne; lallai ne gwamnati tayi humɓasa wajan tashi tsaye tayi tsayuwar tsayin daka wajan bayar da ilimi a cikin al'umma domin jahilci na taka gagarumar gudunmuwa a fannin ta'addanci, haɗi da wayar da kan al'umma akan alfanun zaman lafiya da kuma irin muhimman abubuwan da zaman lafiya ke kawowa a sanadiyar zaman lafiya, hakan zai taimaka matuƙa ainun wajan samun haɗin kan al'umma domin a zauna lafiya.
A ƙarshe ina addu'ar samun dauwamammen zaman lafiya a cikin jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
Daga Nura Muhammad Mai Apple
Comments
Post a Comment