Makomar Najeriya a kasashen duniya a taron koli na majalisar dinkin duniya
KO NAJERIYA TA TABA SAMUN WANI ALFANU A CIKIN TARON DA TAKE HALLARTA A ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA?
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Kamar yadda ake ci gaba da gudanar da ire-iren wadannan tarurruka a shekara-shekara wanda wannan shine 74 a cikin jerin tattaunawar da ake a zauren majalisar dinkin duniya. Najariya Kasa ce Mai albarka kuma tana da kima da daraja a idon duniya Wanda hakan ya sa itama tana daya daga cikin manyan baki masu jawabi a cikin zauren na majalisar.
Taron Wanda yake gudana, kuma manufar taron na bana shine kalubale na sauyin yanayi, Wanda ake kokarin ganin an tallafawa kasashen duniya masu fama da wannan matsalar, kuma a cikin taron har wasu gwamnatocin kasashen duniya sun Fara bayar da tallafinsu a cikin wannan shirin, shirin Wanda ya samu bakuntar kasashe 66 a bana.
Shugaban majalisar dinkin duniya Antonio kutaresh
Manyan kasashen da sun kafi kowa morewa tarurrukan Wanda majalisar dinkin duniya take shiryawa 'yan tsiraru ne, daga ciki akwai; Amurka da Rasha, da Japan, da China, da kuma Prance, amma har yanzu Najariya babu wani alfanu da samu ko take samu a cikin tarurrukan.
A jiya ne Shugaban kasar Najariya Muhammadu Buhari yayi cikakken jawabi a wajan taron har na tsawon Mintuna 15:40, duk da kasancewar ya tabo muhimman abubuwa daban-daban, daga ciki harda na neman taimakon kasashen duniya wajan ceto tafkin Chadi Wanda yake cikin barazana, to mu a mahangarmu ta masu nazarin abubuwan yau da kullum, muna ganin ko a wannan Karon haka za'a watse taron ba tare da mun amfana da komai ba, duk da mataimakiyyar Shugaban majalisar Hajiya Amina Muhammad 'yar Najeriya ce, to amma hakan baya saka mata Kishin kasar da kuma tunanen taimaka mata.
Lokacin da shugaba Buhari na Najeriya yake jawabi
A karshe muna fatan taron na wannan Karon zai amfanar da Najeriya, kuma ya sa Tana cikin kasashen da zasu ci moriyar wannan shirin.
Duk wani shiri ba zai yi tasiri ba har sai mu 'yan Najeriya mun hada kanmu a matsayin tsintsiya madauri daya, mun yaki wariyar kabilanci, da rashin son junanmu, mun dawo mun hada Kai mun Samar da zaman lafiya a tsakaninmu, Sannan mu Kai ga kowane irin ci gaba.
Allah ya taimaki Najeriya da masu son ganin ta ci gaba.
Daga Nura Mai Apple, Gusau
Copyright@nuramaiapple2019

Comments
Post a Comment