Skip to main content

Posts

Najeriya Barka da samun 'yancin kai shekara59

Najeriya Kasa mai albarka, hakika muna godiya ga Allah ta'ala da ya nuna mana Najeriya ta cika shekara 59 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniyya, duk wani dan kasa na gari ya zama wajibi yayi murna da wannan rana, domin abun alfahari ce ga 'yan Najeriya kwata. Ya zama wajibi muyi jinjina ga 'yan mazan jiya, wato  Sir Ahmadu Bello Sardaunan sakkwato. Da Sir Abubakar Tafawa ɓalewa, da sauran wadanda lokaci ba zai bani damar zaiyana su ba,  wadannan jajirtattun mutane sun taka muhimmiyyar raya wajen hada kan kasar nan domin kasancewa turba daya, kuma a matsayin tsintsiya madauri daya. Muna addu'ar Allah yayi masu sakayya da gidan al'janna. A bisa wannan ya kamata shuwagabannin wannan zamani suyi kwaikwayon kyakkwan halayen wadannan bayin Allah domin ganin kasar nan ta ci gaba da zama a matsayin turba daya, idan har ana son ganin kasar nan ta cigaba da zama a matsayin abu daya, to lallai ne shuwagabannin kasar su sanya kishin kasa gaba ...

Makomar Najeriya a kasashen duniya a taron koli na majalisar dinkin duniya

KO NAJERIYA TA TABA SAMUN WANI ALFANU A CIKIN TARON DA TAKE HALLARTA A ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA?                Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Kamar yadda ake ci gaba da gudanar da ire-iren wadannan tarurruka a shekara-shekara wanda wannan shine 74 a cikin jerin tattaunawar da ake a zauren majalisar dinkin duniya. Najariya Kasa ce Mai albarka kuma tana da kima da daraja a idon duniya Wanda hakan ya sa itama tana daya daga cikin manyan baki masu jawabi a cikin zauren na majalisar. Taron Wanda yake gudana, kuma manufar taron na bana shine kalubale na sauyin yanayi, Wanda ake kokarin ganin an tallafawa kasashen duniya masu fama da wannan matsalar, kuma a cikin taron har wasu gwamnatocin kasashen duniya sun Fara bayar da tallafinsu a cikin wannan shirin, shirin Wanda ya samu bakuntar kasashe 66 a bana.                 Shugaban majalisar dinkin duniya Antonio kutaresh Manyan kasashen da ...

Zuwa Ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Assalamu alaikum, da fatan alheri ga dukkan wanda zai karanta wannan rubutu nawa, ina fatan wannan rubutu nawa zai kai ga hannun Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Bahari, na dubi yiwuwar wannan rubutun ne domin kara yin tuni ga Muhammadu Bahari akan Arewa, wanda shi kansa ɗan yankin Arewa ne, kuma Arewar tana cikin wani hali, lallai ne ayi duk mai yiwuwa wajan dawo da martabarta. Duk da kasancewar sha'anin mulki abu ne mai matukar sarkakiya da wahalar gaske, duk da kasancewar munsan kana iya ƙoƙarinka wajan ganin kafitar da ƙasar nan ga tudunmun tsira, amma ya kamata a dubi arewa da idon Rahama, ya kamata a samarwa da arewa abubuwa masu matuƙar muhimmancin gaske wanda ko bayan baka a samun kujerar shugabancin ƙasar nan duk lokacin da aka tuna da abubuwan na alheri za'a rika maka addu'a da fatan alheri. Ganin wannan shine wa'adi na ƙarshe ga reka, kuma shine dama ta ƙashe wadda ya kamata kayi amfani da ita wajen maida akalar tunanenka a yankinka, lallai ne a gina...

Ra'ayin mai Apple, a kan masu kokarin tada zaune tsaye

Tsaro; wani babban tsani ne wanda shine ake bi wajan samuwar dukkan abubuwan rayuwa, kuma sai da shine sannan komai na rayuwa yake tafiya daidai, tsaro wani babban ginshiƙi ne a rayuwar al'umma. Babu wata ƙasa a duniya da zata samu ci gaba, ko ta samu ci gaba, ko take cikin samun ci gaba ba tare samuwar zaman lafiya ba. Wannan ne yasa mun ka himmatu wajan gwaggwarmayar ganin jihar Zamfara ta samu sauyi ta fuskar gwamnati a bisa la'akari da yadda waccen gwamatin da ta shuɗe ta gaza matuƙa ainun wajan kare rayukan al'umma haɗi da dukiyoyinsu, mun ka tsaya kai-da-fata wajan ganin an samu kyakkyawan sauyi domin al'ummar jihar Zamfara su riƙa kwana da idanu biyu-biyu ba tare da wani ɗar a zuciya ba. Kuma cikin ikon Allah, sai da muka ga haƙarmu ta cimma ruwa a wannan fannin. Wannan ne yasa mun ka koma gyefe daya munka zura idanu muna kallon kamun ludayin wannan gwamatin kasancewar mun ga da gaske take wajan samar da tsaro a cikin kwaryar jihar Zamfara haɗi da wasu ma...

Babban taron kungiyar Remarkable Karo na Hudu ya kayatar

              'ya'yan kungiyar remarkable bayan kammala taro. _Wannan kungiya mai suna a sama tayi taronta kamar yadda ta saba, kuma an kammala cikin nasara da kwanciyar hankali, an tattauna akan muhimman abubuwa masu matukar amfani ga Al'umma Musamman marasa gata._ _Daga cikin ayyukan da kungiyar za ta maida hankali a Kai shine tallafawa al'majirai masu karatun allo, don ba da gudumuwa ga abinda ya shafi addini. Bayan kammala hakan daidai iyawarmu da kuma karfinmu,  Abu na gaba shine kungiya zata zagaya domin gaisuwar ban girma hadi da neman shawarwari ga dattawan kungiyar don a gudu tare a tsira tare._                  Shugaban kungiyar tare malamin jami'a na birnin kebbi         _Idan ba son juna hadin Kai da wuya kaga ya dore, ko shakka babu yana da kyau mu kasance masu hadin Kai da nuna kishi wa junanmu, hakan zai bamu damar cin kowace irin nasara, dole ne mu nis...

RUGUNTSUMIN CHANZA SHEKA; hattara Zamfarawa da 'yan yaudara.

RUGUNTSUMIN CHANZA SHEKA; hattara Zamfarawa da 'yan yaudara. Wani abu da ba kasafai ake yinsa ba kafatanin duniya kwata, inda banda Afrika musamman Najeriya, shine ribibin chanza sheka daga wannan jam'iyyar siyasa zuwa waccan, musamman idan aka samu chanjin gwamnati. Wasu suna daukar abun tamkar kasuwanci ko zuba jari a kasuwa, hakika wannan tunane, ko nace irin wannan safgar/ siga ta sha bam-ban da wasu kasashen duniya. Idan muka yi nazari da kyau muka dubi kasar Amurka wadda ita ce Najeriya take kwaikwayo a falsafar tafiyar da al'amurran yau da kullum, musamman a fagen siyasa hadi da daftarin demokaradiyya, a kasar Amurka duk da yawan da take da shi da kuma fintikau da tayiwa wasu kasashen duniya, Amma jam'iyyun siyasar su biyu,  Publican da kuma Democratic, kuma sune suke ci gaba da mulkar kasar tun farkon samun 'yancin gashin kai har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Bari dai kar na wahalar da Mai karatu, kachokan bari naje wajen abinda nake son cewa domin ...

Makomar mabiya mazhabar shi'a a Najeriya

Babu shakka, kowa yasan Najeriya ya san Kasa ce mai yawan addinai daban-daban sannan kundin tsarin mulki na kasa a Najeriya yaba kowane addini damar yin addininsa ba tare da tsangwama, ko hantara ba, matukar ba yazo da wani abu wanda zai ci karo da saɓa Ƙa'ida ba, Najeriya ƙasar da ta baiwa dukkan 'yan ƙasar cikakkiyar damar ci gaba da rayuwa a cikin ƙasar ba tare da wani fargaba, ko shakku ba.                    lokacin da suke zanga-zanga a Abuja Tun lokacin da aka samu karon batta a tsakanin sojojin Najeriyar da 'ya'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta mabiya mazhabar shi'a a shekarar 2015 a birnin Zaria ta jihar Kaduna, ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula har zuwa wannan lokaci da muke ciki, rikicin wanda yayi sanadiyar ajalin gwamman rayuka haɗi da dukiyoyi, wani babban abun takaici ne da Allah waddai. Kuma yana daya daga cikin abinda ya mayar da hannun agogo baya, ta fuskar ƙoƙarin da ake wajen ganin ƙasar nan ta samu d...