RUGUNTSUMIN CHANZA SHEKA; hattara Zamfarawa da 'yan yaudara.

RUGUNTSUMIN CHANZA SHEKA; hattara Zamfarawa da 'yan yaudara.

Wani abu da ba kasafai ake yinsa ba kafatanin duniya kwata, inda banda Afrika musamman Najeriya, shine ribibin chanza sheka daga wannan jam'iyyar siyasa zuwa waccan, musamman idan aka samu chanjin gwamnati. Wasu suna daukar abun tamkar kasuwanci ko zuba jari a kasuwa, hakika wannan tunane, ko nace irin wannan safgar/ siga ta sha bam-ban da wasu kasashen duniya.

Idan muka yi nazari da kyau muka dubi kasar Amurka wadda ita ce Najeriya take kwaikwayo a falsafar tafiyar da al'amurran yau da kullum, musamman a fagen siyasa hadi da daftarin demokaradiyya, a kasar Amurka duk da yawan da take da shi da kuma fintikau da tayiwa wasu kasashen duniya, Amma jam'iyyun siyasar su biyu,  Publican da kuma Democratic, kuma sune suke ci gaba da mulkar kasar tun farkon samun 'yancin gashin kai har zuwa wannan lokaci da muke ciki.

Bari dai kar na wahalar da Mai karatu, kachokan bari naje wajen abinda nake son cewa domin Mai karatu ya fahimci inda na Mai da gaba.

Ina magana ne a kan jihar Zamfara, tun farkon samun assasa wannan jihar tana daya daga cikin Jihohin da suke fama da farfagandar siyasa, ko da yake wannan ne Karo na farko da aka samu juyin-juya-halin siyasa a jihar ta Zamfara. Inda jam'iyyar PDP ta samu damar karɓe ragamar jagorancin shugabancin jihar.


       Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya


A gida irin na siyasa dole ne a samu mutane masu tsantseni domin hakan ne zai bada damar cimma dukkanin nasarar da ake buƙata, wajan fafutikar da ake don ganin a ciyar da jiha gaba.

To sai dai wani abin mamaki shine irin yadda wasu jiga-jigan waccan tsohuwar tafiyar suka fara juya akalarsu daga waccen tafiyar zuwa wannan. kuma sune suka san ciki da wajen waccan tsohowar gwamnatin, yanzu kuma sune suka fara juyowa suna dawowa cikin tafiyar wannan gwamnati, sannan ana karɓarsu ba tare da bin diddigin shin a lokacin da suna cikin waccen tafiyar ta tsohowar gwamnatin da ta shuɗe wace irin gudunmuwa suka baiwa al'umma, wadda kuma yanzu suke ganin suɓulewar damar ne ya sa su waiwaye domin su dawo cikin wannan tafiyar don ganin an ciyar da jiha a gaba.


Yana da kyau Gwamnatin jihar Zamfara da tayi dogon nazari akan masu ribibin sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata musamman a jam'iyyar dake riƙe da madafun iko, don gudun yin kisto da kwarkwata, duk wani mai muradin kawo sauye-sauye a cikin al'umma zai iya bada kowace irin gudunmuwa ba kawai sai a jam'iyyar da ke mulki ba.

Tabbas daga cikin kowace al'umma akwai ɓata gari, musamman 'yan ɓata miya ba don asha ba.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin mai girma Gwamnan Jihar Zamfara (Rt Hon Bello Muhammad m.o.n Matawallen Maradun) da yayi taka tsantsan wajen shigar wasu cikin gwamnatinsa, saboda ganin irin yadda ya dauko tsare-tsare masu ma'ana, don ganin jihar nan ta samu cigaba ta kowane fanni.

A karshe ina addu'ar samun zaman lafiya mai dorewa a jihar Zamfara da Arewacin Najeriya da Najeriya da Duniya baki daya. Fatan alheri ga Gwamnatin Matawalle.


Comrd Nura Muhammad mai Apple Gusau 081333376020




Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’