Skip to main content

Babban taron kungiyar Remarkable Karo na Hudu ya kayatar



              'ya'yan kungiyar remarkable bayan kammala taro.


_Wannan kungiya mai suna a sama tayi taronta kamar yadda ta saba, kuma an kammala cikin nasara da kwanciyar hankali, an tattauna akan muhimman abubuwa masu matukar amfani ga Al'umma Musamman marasa gata._

_Daga cikin ayyukan da kungiyar za ta maida hankali a Kai shine tallafawa al'majirai masu karatun allo, don ba da gudumuwa ga abinda ya shafi addini. Bayan kammala hakan daidai iyawarmu da kuma karfinmu,  Abu na gaba shine kungiya zata zagaya domin gaisuwar ban girma hadi da neman shawarwari ga dattawan kungiyar don a gudu tare a tsira tare._

                 Shugaban kungiyar tare malamin jami'a na birnin kebbi
       

_Idan ba son juna hadin Kai da wuya kaga ya dore, ko shakka babu yana da kyau mu kasance masu hadin Kai da nuna kishi wa junanmu, hakan zai bamu damar cin kowace irin nasara, dole ne mu nisanci bayyana sirrin kungiyar a individuals domin mu kasance masu fada da cikawa a kan irin manufofi da kuma tsare-tsare da sauye-sauyen wannan kungiya, hakan zai sa Al'umma Su gane bambancin Dan duma da kubewa ! bambancin wannan kungiya da sauran kungiyoyin (NGO) na daban._


_Kasancewar kungiyoyi barkatai suna amfani da lambar yabo ta girmamawa a matsayin bayarwa ga wasu individuals domin neman wani abu ko neman suna da sauransu. Wanda kuma hakan ya sha  bam-ban da kungiyar (Reya) domin ita na ta tsarin ba haka zai kasance ba._


_Wasu daga cikin ayyukan da wannan kungiya ke shirin aiwatarwa kuma zasu kasance daya-bayan-daya akwai;_

_1 Ciyar da almajirai (Almajiran-malam)_

_2 Akwai buga litattafai masu dauke da tambari (logo) da sunan kungiyar (Reya) domin rabawa ga makarantun Primary school da Secondary school. A cikin rabon littafan za'a dubi dalibban da suka fi kowa kokari a cikin classic,  sai kuma wadanda sun ka fi tsafta a cikin Class,  da kuma masu sammakon zuwa makaranta, wadannan sune zasu amfana da shirin domin Kara karfafa musu kwarin gwiwar ci gaba da karatu, da kuma muhimmancin neman ilimi._

_Akwai duba batun ziyartar gidan yari domin zakulo wadanda kananan basussuka suka Kai su a gidan a biya masu domin sahalimusu su dawo cikin jama'a kamar kowa._


_A bisa manufofin wannan kungiya mai albarka, kuma na alheri, akwai bukatar jajircewa, domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya! Saboda haka kungiyar ta na neman hadin kan 'ya'yanta, domin zama tsintsiya madauri daya._



_Mun fitar da takardar cikewa domin tabbatar da matsayinka/ki  a cikin wannan kungiya wato form akan kudi Naira 500 kacal Sannan kowa zai siya tun daga kan shuwagabannin kungiyar da membobinta, hadi da masu sha'awar shiga._

_Ana sayar da wannan form din ne a wajen jami'in Hulda da jama'a na wannan kungiya, *Nura Mai Apple*_ 


_Wadannan sune kadan daga cikin manufofinmu,  muna fatan Allah ya taimakemu ya muna jagora ya bamu ikon tabbata akan gwagwarmaya Mai amfani ga Al'umma._


*Daga Nura Muhammad Mai Apple. P. R. O 1*

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...