Ra'ayin mai Apple, a kan masu kokarin tada zaune tsaye
Tsaro; wani babban tsani ne wanda shine ake bi wajan samuwar dukkan abubuwan rayuwa, kuma sai da shine sannan komai na rayuwa yake tafiya daidai, tsaro wani babban ginshiƙi ne a rayuwar al'umma. Babu wata ƙasa a duniya da zata samu ci gaba, ko ta samu ci gaba, ko take cikin samun ci gaba ba tare samuwar zaman lafiya ba.
Wannan ne yasa mun ka himmatu wajan gwaggwarmayar ganin jihar Zamfara ta samu sauyi ta fuskar gwamnati a bisa la'akari da yadda waccen gwamatin da ta shuɗe ta gaza matuƙa ainun wajan kare rayukan al'umma haɗi da dukiyoyinsu, mun ka tsaya kai-da-fata wajan ganin an samu kyakkyawan sauyi domin al'ummar jihar Zamfara su riƙa kwana da idanu biyu-biyu ba tare da wani ɗar a zuciya ba.
Kuma cikin ikon Allah, sai da muka ga haƙarmu ta cimma ruwa a wannan fannin. Wannan ne yasa mun ka koma gyefe daya munka zura idanu muna kallon kamun ludayin wannan gwamatin kasancewar mun ga da gaske take wajan samar da tsaro a cikin kwaryar jihar Zamfara haɗi da wasu makwaftan jihar, ƙokarin gwamna (Rt. Hon Bello Muhammad Mon Matawallen Maradun) na jihar Zamfara wajan samar da tsaro a jihar Zamfara abun yabawa ne, kuma dole a jinjina masa a wannan fannin.
Duk wani Bazamfare yaji matuƙar daɗi lokacin da yaga zaman lafiya yana gudana, wannan ne yaja hankulan talakawa a sassa daban-daban na jihar ta Zamfara da wasu jihohi damin yiwa gwamna addu'o'i na musamman, don samun ɗorewar zaman lafiya a jihar ta Zamfara da Arewa da Najeriya baki daya.
To sai dai kokarin wasu ɓata gari masu son maida hannun agogo baya, na son tada zaune tsaye, a sha'anin tsaron wani babban abun takaici ne, haɗi da tir da Allah waddai, kuma ya kama su san cewa Allah ya la'anci duk mai tada rigima da hargitsi a cikin al'umma, yana da kyau da muhimmanci muji tsoron Allah a cikin kowane irin al'amari na rayuwa, ya zama wajibi mu haɗa kai domin zaman wanzuwar zaman lafiya a cikinmu, hakan zai yi tasiri wajan bunkasuwar jiharmu ta Zamfara har mu ciyar da wasu jihohi da dama na ƙasar nan.
Ƙalubalenku jami'an tsaro, lallai ne kuyi iya ƙokarinku wajan kara tashi tsaye da tanke ɗamarar binciken kwakwaf da amfani da kwarewarku, da hikimarku, wajan zaƙulo bayanan sirri, na masu ƙoƙarin ganin sun banzarantar da tsaro a cikin jahar nan domin su fuskanci fushin hukuma a yanke musu hukunci daidai da abinda sun ka aikata, ko suke ƙokarin aikatawa.
Muna fatan samun dauwamammen Zaman lafiya a jihar Zamfara da Najariya baki daya. Fatan alheri da gwamnati jihar Zamfara.
Daga; Nura Mai Apple
Comments
Post a Comment