Zuwa Ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.



Assalamu alaikum, da fatan alheri ga dukkan wanda zai karanta wannan rubutu nawa, ina fatan wannan rubutu nawa zai kai ga hannun Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Bahari, na dubi yiwuwar wannan rubutun ne domin kara yin tuni ga Muhammadu Bahari akan Arewa, wanda shi kansa ɗan yankin Arewa ne, kuma Arewar tana cikin wani hali, lallai ne ayi duk mai yiwuwa wajan dawo da martabarta.

Duk da kasancewar sha'anin mulki abu ne mai matukar sarkakiya da wahalar gaske, duk da kasancewar munsan kana iya ƙoƙarinka wajan ganin kafitar da ƙasar nan ga tudunmun tsira, amma ya kamata a dubi arewa da idon Rahama, ya kamata a samarwa da arewa abubuwa masu matuƙar muhimmancin gaske wanda ko bayan baka a samun kujerar shugabancin ƙasar nan duk lokacin da aka tuna da abubuwan na alheri za'a rika maka addu'a da fatan alheri.

Ganin wannan shine wa'adi na ƙarshe ga reka, kuma shine dama ta ƙashe wadda ya kamata kayi amfani da ita wajen maida akalar tunanenka a yankinka, lallai ne a gina arewa da abubuwan more rayuwa, da haɓɓaka hulɗar kasuwanci da farfaɗo da manyan kwamfanonin arewa, wanda hakan zaisa dubban matasa su samu ayyukan yi, babu shakka mun san kayi ƙoƙari wajan samar da ayyukanyi ga matasa musamman samar da shirin nan na N-Pawer da sauransu, amma gaskiya hakan ba zai wadatar ba.

Shugaba Bahari ka sani babu wani wanda ya nuna maka soyayya ta gaskiya ta zahiri kamar mutanen Arewa, babu shakka yana da kyau ka mayar musu da biki, har yanzu akwai dubban matasa a arewa waɗanda basu da sana'ar yi, kawai suna zaman kashe wando, wanda hakan babban koma baya ne, shugaban Buhari arewa tana cikin matuƙar buƙatar neman taimakonka.

Shugaba Bahari yana da kyau ka yaye duk wani hijabi dake tsakaninka da talakawanka, domin kaima ka hangosu kamar yadda suma sun kayimaka kara, muna fatan zaka dubi makomar arewa da 'yan arewa, kuma ka gina arewa kafin karshe wa'adin mulkinka, muna fatan Allah yasa ka fahimci irin soyayyar da 'yan arewa sun ka nuna maka, domin share musu hawayensu.


Fatan alheri ga reka da kuma masu son arewa, da kishin mutanen arewa.


Daga Nura Muhammad mai Apple. Gusau 08133376020

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’