Makomar mabiya mazhabar shi'a a Najeriya
Babu shakka, kowa yasan Najeriya ya san Kasa ce mai yawan addinai daban-daban sannan kundin tsarin mulki na kasa a Najeriya yaba kowane addini damar yin addininsa ba tare da tsangwama, ko hantara ba, matukar ba yazo da wani abu wanda zai ci karo da saɓa Ƙa'ida ba, Najeriya ƙasar da ta baiwa dukkan 'yan ƙasar cikakkiyar damar ci gaba da rayuwa a cikin ƙasar ba tare da wani fargaba, ko shakku ba.
lokacin da suke zanga-zanga a Abuja
Tun lokacin da aka samu karon batta a tsakanin sojojin Najeriyar da 'ya'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta mabiya mazhabar shi'a a shekarar 2015 a birnin Zaria ta jihar Kaduna, ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula har zuwa wannan lokaci da muke ciki, rikicin wanda yayi sanadiyar ajalin gwamman rayuka haɗi da dukiyoyi, wani babban abun takaici ne da Allah waddai. Kuma yana daya daga cikin abinda ya mayar da hannun agogo baya, ta fuskar ƙoƙarin da ake wajen ganin ƙasar nan ta samu dauwamammen zaman lafiya haɗi da ci gaban Ƙasa.
To sai dai rikicin kwana-kwanan nan wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, shine mafi munin rikicin da munka gani, ta fuskar amfani da karfin da ya wuce ƙima na son shiga majalisar dattawan Kasar da karfin tuwo, wanda haka yayi sanadiyar mutuwar wani babban jami'in tsaro, haɗi da wani ɗan Jarida. A kan ƙoƙarin mabiya mazhabar shi'ar na son a saki jagoransu Sheikh Ibrahim Alzakkaky. Wanda ake cigaba da tsarewa akan wancen laifin da ake zarginsa da shi na sa magoya bayansa suyi fito-na-fito da hukuma.
Lokacin da suke fito na fito da vyan sanda
Duk wanda yake a cikin kasar nan yasan cewa ɗaukar doka a hannu ba karamin kuskure ba ne, kuma taka doka ne daga cikin dokokin kasa, sanin ya kamata shine mutum ya yi amfani da abubuwa guda biyu, na farko shine; idan ya aikata abu, shin ba laifi bane a cikin addininsa? Na biyu shin abin nan da dan Adam zai aikata shin zaici karo da dokokin ƙasa, babu shakka duk mai amfani da irin waɗannan dabarun babu yadda za'ayi yayi abun tir da Allah waddai, har a ƙarshe ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakinin al'umma.
Kungiyar addini mai fafutikar watsa da'awa a cikin al'umma, basa faɗa ko tashin hankali da juna, duk mai ƙoƙarin ganin da'awarsa ta samu karɓuwa a cikin al'umma yana bi ne sannu a hanhali cikin lumana da kwanciyar hankali cikin tsanaki sannan a natse, domin mutane su gane hikimar da ke akwai a cikin addinin hakan zai kara ƙarfafa ma wasu mutane gwiwa suji suna sha'awar shiga, ba tare da kai ruwa rana ba.
Addinin musulunci bai barmu kara zube ba, ya koya mana yadda zamu yi mu'amala da al'umma daban-daban daga ciki har waɗanda ba addininmu guda da su ba, babu shakka addini musulunci baya ƙirƙirar tashin hankali, ko son rashin zaman lafiya a tsakanin al'umma maban-banta a duk inda mutum ya tsinci kansa.
Saka kungiyar a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda, yana da kyau mahukunta su tsaya suyi karatun ta natsu wajen amfani da dabaru da hikimomi, wajen nazarin hanyar da ya kamata abi, domin ganin yin haka ba zai kara ruruta wata wutar rikici ba, La'akari da yadda muke ganin abun zai shafi arewa ne, idan mukayi dubi mai kyau. Ga kungiyar masu tada ƙayar baya ta 'yan Boko Haram, haka ga ta masu satar shanu wadda ta juya zuwa ta masu garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, sannan yanzu ga rikicin kungiyar mabiya shi'a.
Yanzu lokaci ne da ya kamata a haɗu domin laluɓo hanyoyin samun zaman lafiya, kasancewar shine kashin bayan ci gaba kowace al'umma a duniya, saboda muna maraba da duk wata hanya da gwamnati take ganin ya dace abi domin samun zaman lafiya, muna kira da babbar murya ga 'ya'yan wannan kungiya da su san babu abinda yafi zama lafiya daɗi, sannan yana da kyau mu koyi yadda ake zama lafiya, don mu zauna lafiya har mu ciyar da ƙasar a gaba.
A ƙarshe muna addu'ar Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alheri a cikin ƙasarmu Najeriya baki daya.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment