Skip to main content

Posts

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...

KWACE-KWACEN WAYOYIN AL'UMMA YANA CIGABA DA ƘAMARI A GUSAU!

Ɓata gari masu bibiyar wasu unguwanni suna ƙarɓewa jama'a wayoyin hannu suna cigaba da cin karansu ba babbaka inda yanzu suke cigaba da cikin kasuwarsu da rana kata! Tsotsayi baya wuce ranarsa, wannan ƙaddarar yau ta rutsa da abokinmu Anas Ahmad wanda akafi sani da malam Zanzaro. Da misalin ƙarfe biyar chif-chif saman babban titin sha talen-talen Bello Bara'u kusa da Masallacin Malam Mai Kwano wasu sunka masa fisgen wayoyinsa. A daidai wannan lokaci sanin kowane wayar hannu ta zamarwa al'umma tamkar rabin rayuwa ne, saboda komai mai muhimmanci yana cikinta. Wannan yana zuwa ne duk da gwamnati tace tana sanya ido akan masu yin wannan muguwar sana'ar ta fisgen wayar hannu. Muna fatan gwamnati zata zagen damtse wajen ganin ta daƙile wannan lamari a cikin Gusau kasancewar a nan ne abin yafi ƙamari. Muna roƙon Allah ya tona asirin duk wanda yake irin wannan muguwar ɗabi'a, kuma Allah ya mayarwa da duk wanda irin wannan lamari ya rutsa da shi, da ma...

MU KAWAR DA BARA, DOMIN FARFAƊO DA MARTABARMU A YANKIN AREWA!

Assalamu alaikum, Sannun mu da warhaka Da fatan alheri ga kowa, ko shakka babu illar barace-barace a cikin al'umma illa ce mai matuƙar hatsarin gaske wanda ya kamata mu hada hannu ƙarfi da ƙarfe domin yaƙarta a cikin al'ummarmu domin samarwa da 'yan bayanmu kyakkyawar makoma. Addinin musulunci ya koyar da mu yadda zamu kasance mutane nagari a cikin jama'a a inda duk inda muka shiga za'ayi alfahari da mu a ko ina a faɗin duniyar nan, haka ya koyar damu yadda zamuyi mu'amala da har mutanen da ba addininmu ɗaya da su ba. Ya ku 'yan uwa musulmi! Ko shakka babu musulunci bai yadda da bara ba, sai dai akan lalura, Misali wanda yana cikin hali na tafiya sai guzurinsa ya ƙare, wannan musulunci ya yarje masa yayi bara domin ya samu iya adadin abinda zai isa ya kaishi inda yake son yaje. Sannan wanda yake cikin wani hali na ƙa-ƙa-ni-ka yi, shima wannan an yarje masa yayi bara domin samun ɗan abinda zai tashi da kansa ma'ana ya samu ɗan abun yin sana'...

RA'AYIN MAI APPLE AKAN SIYASAR KANO

Assalamu alaikum, barkarmu da yau barka da wannan lokaci tare da fatan dukan masu bibiya ta a kafofin sadarwa daban-daban suna cikin koshin lafiya, ya a kaji da fama? Yau ra'ayin nawa zai maida hankali ne kachokan akan siyasar wata jiha daga cikin manyan jihohin Najeriya kuma jiha mafi yawan al'umma a Najeriya, wato jihar Margayi malam Aminu Wato Kano kenan. Tabbas jihar kano jiha ce wanda Allah madaukakin sarki ya arzuta ta da mutane masu hazaka da basira da kwazo da sanin ya kamata, sannan kanawa mutane ne, masu kawaici da nuna da'a da dattako. Tun farkon samuwar wannan kasar tamu, wato Najeriya, tun lokacin zamunna daban-daban da suka shude, Jihar kano sananniya ce wajen kokarinta na kawo dukan cigaban da za'ayi alfahari da ita, wanda a cikin jajircewar ta ne yasa Arewa tayi fice kuma ta samu daukaka ƙima da daraja a idon Duniya. Kamar dai yadda masu salon iya zance suke fada da cewa ''Kano Ta Dabo Tunbin Giwa yaro Ko Dame kazo Anfika'' ko shakk...

LABARIN SIRRI...... 'YAN SIYASAR AREWA

Daga; Nura Mai Apple Wasu daga cikin gwamnatocin Arewa Sun ware makuddan kudade domin sayen masu kada kuri'a, domin zarcewa a wa'adi na gaba, ko zarcewar magadan da zasu gadar kujerunsu a matakin gwamna ko 'yan majalisu. Bayanin sirrin ya fara bayyana ne daga wata majiya Mai kyau. Inda gwamnatocin suke amfani da kudaden baitin-malin gwamnati domin kaiwa ga nasarar 'yan takararsu. Ko shakka babu, Amfani da kudi wajen sauya bukatun masu kada kuri'a, wajen amfani da kuncin rayuwa da talaucin da ya addabi 'yan Arewa, wani babban abun koma baya ne ta fuskar demokaradiyyar kasar nan. Ya kamata hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC DA ICPC suyi iya kokarinsu wajen saka ido sosai ga gwamnatocin Arewa, domin dakile wannan gagarumar matsala. Yana daya daga cikin abinda yasa Masu hannu da shuni da 'yan siyasar kasar nan suke kiyayye da magance matsalar talauci a Najeriya. Allah Muna Addu'a da sunaye...

YA KAMATA JAM'IYYUN ADAWA A JIHAR ZAMFARA SU ƘAURACEWA BABBAN ZAƁEN GWAMNONI DA NA 'YAN MAJALISUN JIHA DAKE TAFE

Ko shakka babu; kamar yadda ta bayyana ƙarara a zaɓen da ya gudana na shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisun tarayya a ranar 23 ga fabrairun makon da ya gabata, irin yadda anka samu tarin matsaloli wajen yin zaɓen, Jam'iyyar APC mai ƙarfin fada a ji a cikin jihar ta Zamfara ita tayi uwa, tayi makarɓiya a cikin zaɓen, ma'ana dai ina nufin jam'iyyar tayi amfani da karfin ikon da take da shi, wajen cin karanta ba babbaka a dukkanin inda aka gabatar da zaɓen duk da kasancewar ita shugabar zaɓe ta jihar Zamfara ta tabbatar da za'ayi zaɓe mai cike da sahihanci da tsafta wanda kowa zaiyi na'am da shi. A daidai lokacin da aka wayi garin safiyar zuwa runfunan zaɓe wato ranar Asabar, an samu wasu matsaloli, ta fuskar jinkirin kai kayan zaɓe da wuri, inda wasu rahotannin da muka samu daga wasu jihohin ƙasar nan daban-daban sun dade da fara jefa kuri'unsu, alhali kuma a nan jihar Zamfara ba'a kai kayan zabe ba, duk da tabbacin da hukumar shirya zabe ta ƙasa ta b...

JUYIN JUYA HALIN SIYASAR NAJERIYA YASA SUNAN ZAMFARA YA DUSASHE!

Daga; Nura Muhammad mai Apple, Gusau. Gagarumar ɓaraka, da muhawara mai zafin gaske, da musayar kalamai da suka kaure tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai fafutikar ganin ya koma karagar mulkin Najeriya wa'adi na biyu. Da Madugun 'yan Adawar jam'iyyar PDP Wato Alh. Atiku Abubakar. yasa sunan Zamfara ya 'bace Bat, na inda anka kwana wajen Gwama sunayen 'yan takarar Jam'iyyar Apc Mai Mulki a Jihar Zamfara cikin jerin Jadawalin zaben da zai gudana, 'yan Kwanaki kadan masu zuwa! In ana babbakar Giwa ba'ajin ƙaurin bera. Irin yadda siyasar Kasar ta Ɗauki wani sabon salo, yasa kwata-kwata an daina labarin jihar ta Zamfara, balle musan ina ina aka kwana ta wannan ɓangaren. A gyefe duga kuwa, kamar saka sunayen 'yan takara daga jihar Zamfara zai kara sa dangantakar kara tsami matuƙa ainun, a ɓangarorin jam'iyyun guda biyu. Muna fatan za'ayi siyasa a Najeriya mai tsafta, bada gaba ba.  Muna fata kafin nan da wani ɗan lokaci ...