YA KAMATA JAM'IYYUN ADAWA A JIHAR ZAMFARA SU ƘAURACEWA BABBAN ZAƁEN GWAMNONI DA NA 'YAN MAJALISUN JIHA DAKE TAFE




Ko shakka babu; kamar yadda ta bayyana ƙarara a zaɓen da ya gudana na shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisun tarayya a ranar 23 ga fabrairun makon da ya gabata, irin yadda anka samu tarin matsaloli wajen yin zaɓen, Jam'iyyar APC mai ƙarfin fada a ji a cikin jihar ta Zamfara ita tayi uwa, tayi makarɓiya a cikin zaɓen, ma'ana dai ina nufin jam'iyyar tayi amfani da karfin ikon da take da shi, wajen cin karanta ba babbaka a dukkanin inda aka gabatar da zaɓen duk da kasancewar ita shugabar zaɓe ta jihar Zamfara ta tabbatar da za'ayi zaɓe mai cike da sahihanci da tsafta wanda kowa zaiyi na'am da shi.


A daidai lokacin da aka wayi garin safiyar zuwa runfunan zaɓe wato ranar Asabar, an samu wasu matsaloli, ta fuskar jinkirin kai kayan zaɓe da wuri, inda wasu rahotannin da muka samu daga wasu jihohin ƙasar nan daban-daban sun dade da fara jefa kuri'unsu, alhali kuma a nan jihar Zamfara ba'a kai kayan zabe ba, duk da tabbacin da hukumar shirya zabe ta ƙasa ta bayar na kammala kai kayan zaben a dukkanin lunguna da sakunan jihar ta Zamfara.


Babbar jam'iyyar APCn a jihar Zamfara ta sauyawa talakawan jihar Zamfara  tunane; irin yadda tayi amfani da maƙuddan kudaden Baitil malin gwamnati, wajen siyen masu kada kuri'a ta hanyar baiwa masu kaɗa kuri'a kudi domin zaben jam'iyyar Apc, kasancewar jam'iyyun Adawa a jihar ta Zamfara basu da isasun kuɗaɗen da zasu baiwa al'umma domin jefa musu ƙuri'u.

Duk da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin ƙasa Tu'annati wato EFCC, Ta gargaɗi 'yan siyasa da bada kudade a lokacin da ake gabatar da zaɓuɓɓaka, amma hakan baiyi tasiri ba, damin masu ƙudi sunyi amfani da kudade wajen sayen masu kaɗa kuri'a a lunguna da saƙunan jihar Zamfara.


Kasancewar gwamnati ta tara komai, haƙiƙa za tayi amfani da wannan damar wajen yin abinda taga dama. Kamar yadda ya faru a zaben da ya gudana, 'ko shakka babu hakan zai faru a zaɓe mai zuwa', abisa wannan nake ganin kamar zaifi dacewa jam'iyyun Adawa su ƙauracewa zaben, saboda yana tattare da rashin adalci da aringizo!


Muna Addu'a da fatan Alheri. Ya Allah ka kawoma jihar Zamfara zaman lafiya da aminci da kwanciyar hankali da wadata.

Allah ya taimaki jihar Zamfara da al'ummarta da masu yi mata fatan Alheri baki daya.

Nagode


Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’