Skip to main content

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!



A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta.

A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama.

Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biyu cikin na uku da suka gabata, a lokacin da Gwamnatin jihar Zamfara ta dingi tayar da mutane da sunan sun tare hanya a saman wasu daga cikin titunan Gusau, duk wadanda wannan lamari ya shafa, shin kokasan irin raɗaɗin da sunka ji?

Haka a lokacin da gwamnatin ta Jihar Zamfara ta dingi biyar Tashoshin Mota tana tayarwa da sunan Samar da tsaro a cikin al'umma, ina ganin kamar duk wanda wannan lamari ya shafa baiji daɗi ba, kasancewar akwai dubban jama'a da suke ciyar da iyalansu da 'yan uwansu a ciki, wasu basu da inda suka dogara koma bayan hada-hadar da suke yi a wajen. Dukkanin wanda lamarin ya shafa a wancen lokacin bazaka iya auna irin bakin cikin da ya shiga ba.

Inko haka ne! To ina ga waɗanda hare-haren 'yan Bindiga yasa su arcewa daga garuruwansu zuwa inda basu ma sani ba?

A daidai wannan gabar. Misali; A jihar Borno akwai kungoyin sa kai masu zaman kansu, waɗanda ba mallakar gwamnati ba munga yaddda suke kokari matuka ainun, wajen fafutukar samarwa da al'ummar yankinsu mafita, ta hanyar kokarin nemo tallafi na musamman ga wasu manyan kungiyoyin bada agajin gaggawa na duniya, kuma sunka basu haɗin kai da kwarin gwiwar hada karfi-da-karfe don kawo musu dauki ga al'ummarsu.

A Jihar Borno akwai wurare na musamman da gwamnatin Borno karkashin Jagorancin Gwamna Kashin Shattima ta ware domin kula da 'yan Gudun Hijira. Duk kauyen da tashin hankali ya shafa suna iya zuwa wannan wuri da aka ware dominsu su zauna, su cigaba da da samun tallafi da kulawa da addu'ar samun zaman lafiya a cikin garuruwansu. Duk wanda yake da bukatar bayar da taimako zai iya zuwa wajen domin bayar da taimakon.

Amma mu jihar Zamfara har yanzu 'yan gudun Hijiranmu sun kasa samun irin wannan gata cikin jama'a, ya kamata asan suma fa Mutane ne kamar kowa, sannan suma suna bukatar jin daɗin rayuwa kamar kowa, haka suma ba'ason ransu haka ya faru da su ba, tsautsayi ne wanda baya wuce ranarsa.

Inko haka ne! to meyasa baza'a taimakesu ba? Me yasa baza'a janyo
Su a jiki ba? Ko shakka babu irin kudaden da gwamnatin jihar Zamfara take kashewa duk wunin Allah wajen fannin siyasa da anyi amfani da koda rabinsu, wajen tallafawa 'yan gudun Hijira tabbas za suji dadi, matuƙa duk da damuwar da suke ciki.

Kasancewsr yanzu azumi yana ƙarasowa shin ina makomar waɗannan bayin Allah? Tayaya zasu samu abinda za suci domin samun damar gabatar da ibada cikin sukuni da walwala? Haƙiƙa ya kamata a dubi 'yan gudun hijira da idon rahama a taimaka musu.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Zamfara  da ta dubi girman Allah ta taimaki 'yan gudun hijira da wajen zaman na musamman wato ''Came'' domin samu su tsugunna har Allah ya kawo musu ɗauki a maimakon raɓe-raɓen da suke yi a makarantu ana korarsa. Muna fata hadi da addu'ar Samun dauwamammen Zaman lafiya a cikin jihar Zamfara, da Arewa da Najeriya dama duniyar Musulmai baki daya.

Ya Allah ka karo mana arziki mayinwaci a cikin kasar nan.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara, kuma mai rajin Kare hakkin Dan Adam a Najeriya. Human Rights Defenders and Advocacy  08133376020


Copyright@nuramaiapple






Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...