JUYIN JUYA HALIN SIYASAR NAJERIYA YASA SUNAN ZAMFARA YA DUSASHE!



Daga; Nura Muhammad mai Apple, Gusau.

Gagarumar ɓaraka, da muhawara mai zafin gaske, da musayar kalamai da suka kaure tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai fafutikar ganin ya koma karagar mulkin Najeriya wa'adi na biyu. Da Madugun 'yan Adawar jam'iyyar PDP Wato Alh. Atiku Abubakar. yasa sunan Zamfara ya 'bace Bat, na inda anka kwana wajen Gwama sunayen 'yan takarar Jam'iyyar Apc Mai Mulki a Jihar Zamfara cikin jerin Jadawalin zaben da zai gudana, 'yan Kwanaki kadan masu zuwa!

In ana babbakar Giwa ba'ajin ƙaurin bera. Irin yadda siyasar Kasar ta Ɗauki wani sabon salo, yasa kwata-kwata an daina labarin jihar ta Zamfara, balle musan ina ina aka kwana ta wannan ɓangaren.

A gyefe duga kuwa, kamar saka sunayen 'yan takara daga jihar Zamfara zai kara sa dangantakar kara tsami matuƙa ainun, a ɓangarorin jam'iyyun guda biyu.

Muna fatan za'ayi siyasa a Najeriya mai tsafta, bada gaba ba.

 Muna fata kafin nan da wani ɗan lokaci zamu samu sunaye 'yan Takarar
jam'iyyar Apc a jihar Zamfara, domin fafatawa da su a  babban zabe mai
zuwa.

Allah ya bamu zama lafiya da kwanciyar hankali da wadata.


Copyright@ Mai Apple Gusau

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’