MU KAWAR DA BARA, DOMIN FARFAƊO DA MARTABARMU A YANKIN AREWA!
Assalamu alaikum,
Sannun mu da warhaka Da fatan alheri ga kowa, ko shakka babu illar barace-barace a cikin al'umma illa ce mai matuƙar hatsarin gaske wanda ya kamata mu hada hannu ƙarfi da ƙarfe domin yaƙarta a cikin al'ummarmu domin samarwa da 'yan bayanmu kyakkyawar makoma.
Addinin musulunci ya koyar da mu yadda zamu kasance mutane nagari a cikin jama'a a inda duk inda muka shiga za'ayi alfahari da mu a ko ina a faɗin duniyar nan, haka ya koyar damu yadda zamuyi mu'amala da har mutanen da ba addininmu ɗaya da su ba. Ya ku 'yan uwa musulmi! Ko shakka babu musulunci bai yadda da bara ba, sai dai akan lalura, Misali wanda yana cikin hali na tafiya sai guzurinsa ya ƙare, wannan musulunci ya yarje masa yayi bara domin ya samu iya adadin abinda zai isa ya kaishi inda yake son yaje.
Sannan wanda yake cikin wani hali na ƙa-ƙa-ni-ka yi, shima wannan an yarje masa yayi bara domin samun ɗan abinda zai tashi da kansa ma'ana ya samu ɗan abun yin sana'a wanda da zarar ya samu to babu shakka bakin nan baran ya haramta gare shi.
ALLAH Maɗaukakin Sarki Yace; "Mun Karrama 'yan Adam" To ashe ko ya za'ayi mu maida kanmu ƙasƙantattu?
A bisa illar da ke akwai a cikin bara, Manzon Allah (S.A.W) ya bamu labari, duk wanda kayin bara kuma har ya Mutu bai tuba ba, a ranar al'ƙiyama zai tashi bashi da naman fuska. mana'a fuskarsa zai tashi da ita ta koma ƙwaranƙwal. Haƙiƙa wannan zai nuna mana illar yin bara domin mu guje Ta mu zauna lafiya da aminci.
Dukan ɗan Adam Akwai baiwar da ALLAH Maɗaukakin Sarki ya yi masa, kuma ya arzutashi da ita cikin iyawarsa da hikimarsa.
Illolin da ke akwai a cikin bara suna da matuƙar yawan gaske wasu daga ciki;-
Yin Bara yana zubarwa da ɗan Adam da mutunci ga idanun al'umma, kasancewar idon mukayi dubo da irin kallon da ake masa, mai naƙasassar Zuciya.
Yin Bara har kullum yana kara sanyawa ɗan Adam Sanyin zuciya wajen rashin kwarin gwiwar tashi ya nemi na kansa, domin cirewa kansa takaici.
Al'ummomi daban-daban a sassa daban-daban na Duniya babu wata al'ummar da babu naƙasassu a cikinta, sannan babu wata ƙasa a duniya da ba ta da marasa ƙarfi, duk da haka basu aminta da yin bara ba, sun dogara ga ALLAH kuma shi yake ciyar da su.
Idon muka dawo a nan cikin gida Najeriya, sai muyi duba a kan wasu daga cikin yankunan Kudancin ƙasar nan, musamman waɗanda ba musulmai ba, za mu ga cewa akwai naƙasassu sosai a cikinsu, amma basu yarda da yin bara ba, amma sun aminta da sana'a komai ƙanƙantarta!
Babbar musifa ce irin yadda a kullum zaka ga 'yan uwanmu a saman tinuna suna tangararo da sunan bara. babban abun damuwa ne irin yadda sunka zubar da martabarmu ga idanun wasu da sunan bara. Babban koma baya ne mu rungumi sana'ar bara, mu zubar da Baiwar da ALLAH yayi mana. Babbar matsala ce mu kasa godiya ga duk halin da munka tsintsi kanmu. Babbar barazana ce a Arewa yin bara.
Muna fatan Gwamnatin tarayyar Najeriya Ƙarƙashin jagoranci mai daraja ta farko a cikin ƙasar nan, kuma mai faɗa aji wato Shugaba Muhammadu Buhari, haɗi da gwamnonin Arewa, da hukumomin Gwamnati da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, su zaburo wajen kauda bara a cikin ƙasar nan, domin samarwa da 'yan baya kyakkyawar rayuwa.
Naƙasa ba kasawa ba! Bara ƙasƙanci ne! Mu kawar da bara domin mu samu salama!
ALLAH bai yimu Ƙasƙantattu ba, Balle mu ƙasƙance!!!
Daga Nura Mai Apple Gusau Ɗan Ƙungiyar Mukawar da Bara ta Kasa Reshen Jihar Zamfara +2348133376020
Copyright@maiapplegusau
Comments
Post a Comment