RA'AYIN MAI APPLE AKAN SIYASAR KANO
Assalamu alaikum, barkarmu da yau barka da wannan lokaci tare da fatan dukan masu bibiya ta a kafofin sadarwa daban-daban suna cikin koshin lafiya, ya a kaji da fama?
Yau ra'ayin nawa zai maida hankali ne kachokan akan siyasar wata jiha daga cikin manyan jihohin Najeriya kuma jiha mafi yawan al'umma a Najeriya, wato jihar Margayi malam Aminu Wato Kano kenan. Tabbas jihar kano jiha ce wanda Allah madaukakin sarki ya arzuta ta da mutane masu hazaka da basira da kwazo da sanin ya kamata, sannan kanawa mutane ne, masu kawaici da nuna da'a da dattako.
Tun farkon samuwar wannan kasar tamu, wato Najeriya, tun lokacin zamunna daban-daban da suka shude, Jihar kano sananniya ce wajen kokarinta na kawo dukan cigaban da za'ayi alfahari da ita, wanda a cikin jajircewar ta ne yasa Arewa tayi fice kuma ta samu daukaka ƙima da daraja a idon Duniya. Kamar dai yadda masu salon iya zance suke fada da cewa ''Kano Ta Dabo Tunbin Giwa yaro Ko Dame kazo Anfika'' ko shakka babu wannan haka yake.
Tun kafin zuwan siyasa a Najeriya, turawan mulkin mallaka sun samu Kano zaune da mutanenta lafiya lau, sannan koda siyasar ta isko mutanen jihar Kano suna da kyakyawar mu'amala da juna a tsakaninsu, suna taimakekeniya da junansu, suna son junansu, hasalima ma, wanda ba'a kano yake ba, bazai gane sirrin mutanen Kano ba, dalili kuwa shine, sun zama tamkar 'yan uwan juna.
Babu ko shakka, Sagegeduwar siyasar wannan zamani tana kokarin ruguza jihar Kano da mutanenta, duba da yadda siyasa ta shiga cikin al'ummar jihar take kokarin daukar wani sabon salo, wanda babu inda zai kai jihar sai tabarbarewa, Allah ya kyauta bama fatan hakan ya kasance, domin jihar Kano itace Arewa. Ko shakka babu, irin abinda yake faruwa a yanzu a jihar Kano saboda siyasa, abun tir da Allah waddai ne, kuma abu ne wanda duk wani dan Arewa mai son cigaban Arewa ɗan kishin al'ummar Arewa, zaiyi bakin ciki da shi matuka ainun.
Dama wasu makiya Arewar, hadi da wasu daga cikin gurbatattun al'ummar Arewa sun kasa lalubo hanyoyin da zasuyi amfani da su wanje wargaza Jihar Kano, shine sunka fake da siyasa suna cin karensu ba babbaka. Hakika wasu daga cikin Matasan jihar kano sun bamu kunya kuma sun bamu mamaki, irin yadda wasu tsirarun mutane sunka hada kai dasu, sunka basu dan abinda bai taka kara ya karya ba domin su tada husuma su illata da raunata 'yan uwansu na jini, waɗanda suke da matukar amfani ga resu.
Ko shakka babu, irin abinda ya faru a jihar kano ya mayar da hannun Agogo baya na sambarka da ake ganin ansamu wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin jihar, kuma ya warware duk wani yarjejeniyar zaman lafiyar da anka kulla, wajen yin zabe a bisa zaman lafiya da lumana, da yin zabe a bisa tsafta.
Muna amfani da wannan damar domin yin kira ga al'ummar jihar Kano da babbar murya da su dubi yiwuwa rungumar zaman lafiya da kaunar juna a tsakaninsu, domin farfado da martabar jiharsu da kuma kimar Wannan yankin namu na Arewa Mai albarka.
Muna fatan Hukumomin tsaro a jihar Kano za suyi binciken kwakwab domin zakulo matasan da sun kayi aika-aikar zubar da jinin mutane hadi da raunata wasu, domin gurfanar da su a gaban kuliya, Don zartar musu da hukunci daidai da laifin da sunka aikata, domin hakan ya zama izina ga wasu masu kokarin aikata hakan a nan gaba.
Babu wata Kasa ko Al'ummar Kasar da zasu cigaba matukar babu zaman lafiya da kaunar juna, muna fata hadi da Addu'ar Allah ya kawo mana zaman lafiya Mai dorewa a jihar Kano da Arewacin Najeriya da Najeriyar dama duniyar musulmai baki daya.
Mun gode
Daga Nura Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment