LABARIN SIRRI...... 'YAN SIYASAR AREWA
Daga; Nura Mai Apple
Wasu daga cikin gwamnatocin Arewa Sun ware makuddan kudade domin sayen masu kada kuri'a, domin zarcewa a wa'adi na gaba, ko zarcewar magadan da zasu gadar kujerunsu a matakin gwamna ko 'yan majalisu.
Bayanin sirrin ya fara bayyana ne daga wata majiya Mai kyau. Inda gwamnatocin suke amfani da kudaden baitin-malin gwamnati domin kaiwa ga nasarar 'yan takararsu.
Ko shakka babu, Amfani da kudi wajen sauya bukatun masu kada kuri'a, wajen amfani da kuncin rayuwa da talaucin da ya addabi 'yan Arewa, wani babban abun koma baya ne ta fuskar demokaradiyyar kasar nan.
Ya kamata hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC DA ICPC suyi iya kokarinsu wajen saka ido sosai ga gwamnatocin Arewa, domin dakile wannan gagarumar matsala.
Yana daya daga cikin abinda yasa Masu hannu da shuni da 'yan siyasar kasar nan suke kiyayye da magance matsalar talauci a Najeriya.
Allah Muna Addu'a da sunayenka masu tsarki da kada ka bada mulki ga Wanda yake kokarin ganin bayan talaka a kasar nan.
Comments
Post a Comment