KWACE-KWACEN WAYOYIN AL'UMMA YANA CIGABA DA ƘAMARI A GUSAU!





Ɓata gari masu bibiyar wasu unguwanni suna ƙarɓewa jama'a wayoyin hannu suna cigaba da cin karansu ba babbaka inda yanzu suke cigaba da cikin kasuwarsu da rana kata!

Tsotsayi baya wuce ranarsa, wannan ƙaddarar yau ta rutsa da abokinmu Anas Ahmad wanda akafi sani da malam Zanzaro.

Da misalin ƙarfe biyar chif-chif saman babban titin sha talen-talen Bello Bara'u kusa da Masallacin Malam Mai Kwano wasu sunka masa fisgen wayoyinsa.

A daidai wannan lokaci sanin kowane wayar hannu ta zamarwa al'umma tamkar rabin rayuwa ne, saboda komai mai muhimmanci yana cikinta.

Wannan yana zuwa ne duk da gwamnati tace tana sanya ido akan masu yin wannan muguwar sana'ar ta fisgen wayar hannu.

Muna fatan gwamnati zata zagen damtse wajen ganin ta daƙile wannan lamari a cikin Gusau kasancewar a nan ne abin yafi ƙamari.


Muna roƙon Allah ya tona asirin duk wanda yake irin wannan muguwar ɗabi'a, kuma Allah ya mayarwa da duk wanda irin wannan lamari ya rutsa da shi, da mafificin alheri.


Daga Nura Mai Apple

Copyright@Nuramaiapple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’