Makomar mabiya mazhabar shi'a a Najeriya
Babu shakka, kowa yasan Najeriya ya san Kasa ce mai yawan addinai daban-daban sannan kundin tsarin mulki na kasa a Najeriya yaba kowane addini damar yin addininsa ba tare da tsangwama, ko hantara ba, matukar ba yazo da wani abu wanda zai ci karo da saɓa Ƙa'ida ba, Najeriya ƙasar da ta baiwa dukkan 'yan ƙasar cikakkiyar damar ci gaba da rayuwa a cikin ƙasar ba tare da wani fargaba, ko shakku ba. lokacin da suke zanga-zanga a Abuja Tun lokacin da aka samu karon batta a tsakanin sojojin Najeriyar da 'ya'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta mabiya mazhabar shi'a a shekarar 2015 a birnin Zaria ta jihar Kaduna, ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula har zuwa wannan lokaci da muke ciki, rikicin wanda yayi sanadiyar ajalin gwamman rayuka haɗi da dukiyoyi, wani babban abun takaici ne da Allah waddai. Kuma yana daya daga cikin abinda ya mayar da hannun agogo baya, ta fuskar ƙoƙarin da ake wajen ganin ƙasar nan ta samu d...