A dakatar ko a tsaftacce sana'ar fina-finan hausa




Yana da kyau gwamnatin Najeriya ta dubi yiyuwar dakatar da sana'ar fina-finan hausa la'akari da yadda take taka rawa wajen gurɓacewar tarbiyyar malam Bahaushe. Ko a dauki matakai na musamman da suka kamata wajen tsaftacceta. mafi yawa daga cikin abubuwan al'ajabi da suke wakana a daidai wannan lokaci, ana kwaikwayon kaso mai tsoka daga cikin fina-finan da ake kallo.


Babbar barazanar da hakan ke haifarwa akwai ƙoƙarin jinginar da al'adar hausawa, haɗi da shi go da wasu baƙin al'adu da suka ci karo da addinin Musulunci ta sigogi mabanbanta.

Irin yadda aka san malam bahaushe da kunya da kamun kai da nuna halin dattako da ɗa'a ga har waɗanda ba kabilarsa ba, amma hakan yana shirin ɓacewa ɓat ! Saboda shigowar wasu baƙin al'adu da muke kalla a cikin fina-finai, yana da matuƙar alfanu a dubi wannan gagarumar matsala.


Mafi yawa daga cikin kaso mai tsoka na fina-finan hausa basu koyama al'umma yadda ake tarbiyya, sai dai nuna yadda ake lalata ta.


Babban abun taikaici ne ace mace bahaushiyya tana iya daukar makami da niyar hallaka abokin zamanta, ma'ana mijinta ko abokiyar zamanta, ba ta tunanin makomarta a matsayinta na musulma, kuma mace wadda ake tunanen samun tarbiyya daga wajenta.

A nan ina magana ne ga fina-finai na hausa kawai, saboda sune namu, kuma ake sarrafawa a cikin mu, kuma kamar yadda suke faɗa suna yi ne, domin inkiya, ko hannunka mai sanda, ko nuni, ko izina a kan faruwar wani abu. Muyi nazari akan illar ba wai abinda ake samu cikinta ba.


Muna kira da babbar murya ga maga'isa da su dubi wannan lamari, kuma suyi nazari a kai domin samun mafita, idan har hana hakan ba zai samu ba, lallai ya kamata a tsaftacceta, domin samun gyaruwar al'umma.

 Nura Mai Apple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’