RASHIN SAMUN ALBASHI MA'AIKATA SUN KOKA
Rayuwar ma'aikacin gwamnati a Najeriya kamar rayuwar hannu baka hannu gwarya ce. mafi yawa daga cikin ma'aikatan gwamnati a wasu sassan Najeriya albashin nasu kawai sun ka dogara da shi, sannan ga tarin iyalai da 'yan uwa, ga sauran dawainiyar yau da kullum, sannan uwa uba ga yanayin kasar yadda take da tsadar rayuwa.
A jihar Zamfara mafi yawa daga cikin ma'aikatanta kachokan sun dogara ne da aikin gwamnati kawai, ga tarin iyalai da 'yan uwan ma'aikatan dakkanin dawainiyarsu sun jingina ta ga aikin na gwamnati.
Tun ana 20 wata ya kare ma'aikaci yake ta zumudin ganin karshen wata don ya anshi albashinsa, kasancewar duk lokacin da albashin zai zo 'yan kudaden albashin lassafaffi ne. 25 ga wata, ma'aikaci da zarar kararrawar wayarsa ta buga, yakan za bura ya duba domin ganin irin sakon da ya shigo a cikin wayar tasa.
Cikin ikon Allah yau 4 ga wata ma'aikacin gwamnati a jihar Zamfara bai amshi albashi ba. Ma'aikata da dama da na zanta dasu, sun bayyana min irin radadin da suke ji, sakamakon rashin shigowar albashin a hannu.
Wani bawan Allah da ya nemi na sakaya sunansa, ya bayyana min cewa iyalansa suna cikin halin ka-ka-ni-ka-yi sakamakon rashin albashin da yake saran zuwansa tun kafin karewar watan da ya gabata. Yace; ''wannan albashin shine kawai abinda na dogara da shi, banda wani abu ko wani kasuwanci da nake yi, bayan aikin gwamnati, na " basusuka da yawanl"l gaske, ina jiran albashin don na biya na kara karbar wasu, amma hakan ya citura''.
Duk da munsan gwamnati tana iya kokarinta wajen inganta walwala da jin dadin al'umma, to amma yana da kyau a dubi matsalar rashin biyan albashin ma'aikata da wuri don magance matsalar.
Muna fatan al'umma zasu samu ingantacciyar rayuwa a cikin wannan manufofi da gwamnatin PDP wadda ta kama aiki cikin watan jiya ke shirin ganin an samu.
Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.
Comments
Post a Comment