Skip to main content

'YAN AREWA MU HAƊA KANMU!

Daga Nura mai Apple

Assalamu alaikum, 'ƴan uwa da abokan arziki barka da yau da wannan lokaci da fatan alheri.

Matashiya; haƙiƙa duk wata al'umma a duniya tana samun cikakken cigaba ne ta fuskar haɗin kai da kaunar juna, tare cire bambance-bambance kabila ko addini ko yare, wannan ne babban matakin kaiwa ga kowace irin nasarar rayuwa da samun dukkanin ci gaban da ake buƙata mai ma'ana.

Tun lokacin da ƙasar Najeriya ta zama ƙasa mai cin gashin kanta, yankin Arewa ya taso da manyan mutane yan gwaggwarmayar ganin yankin ya samu duk wani cigaba dan ganin ya zarce tsara. Haƙiƙa Allah yaji ƙan mazan jiya su Sardauna Gamji ɗan kwarai irin albarka, da Sir Abubakar tafawa Ɓalewa, tabbas waɗannan bayin Allah duk mai bibiyar tarihin su yasan cewa sun bada dukkanin gudunmuwa don ganin cigaban Arewa. Duk mai bibiyar tarihin waɗannan bayin Allah yasan sun yiwa ƙasa hidima ta fuskoki da dama, sun bayar da lokacinsu, da dukiyarsu, da rayuwarsu don kwato yankin arewa ya zama mai faɗa aji, kuma mai cikakken iko a duk faɗin Najeriya.

Idan da a ce waɗannan bayin Allah Suna raye, to ko baƙin cikin irin halin da Arewa ta faɗa yana iya gamawa da su. Saboda faɗawar yankin a hannun marasa kishinta, masu son arzita kansu da iyalansu da 'yan uwansu.

Rashin haɗin kanmu shine babban jigon yin ƙafar ungulu ga duk wani shiri da aka yunƙuru za'a yiwa wannan yankin domin samun maslaha, zaman lafiya da kwanciyar hanhali a tsakanin al'umma.

 Gamu da manyan mutane masu manyan muƙamai amma sun zama manya  wofi, domin babu wani abun cigaba da suke yiwa arewar sai neman a haɗa kai da su a zalunci al'ummar yankin don kawai wani neman tara dukiya ko ta haƙin ƙaƙa!

Duk wani ɗan ƙasa nagari mai son ganin cigaban ƙasar, yana fafutikar kawo wani babban abun cigaba wanda al'ummarsa za suyi alfahari da shi, kuma suyi masa addu'a a duk lokacin da sunka tuna da shi, ko bayan wafatinsa.

Idan mukayi la'akari da waɗannan bayin Allah waɗanda na ambata tun da farko, ai ba ƙuɗi sunka baiwa al'umma ba, a'a. Sun yiwa al'umma aiki ne wanda gashi har gobe ana tunawa da su, kuma ana gode musu akan gwaggwarmayar da suka yi ga jama'arsu, kasancewar basu nuna bambancin ƙabila, ko yare, ko jinsi ba.

Wajibine gwamnonin Arewa da manyan mutane masu riƙe da manyan muƙamai a arewa su haɗa kansu don kawo cigaba mai amfani ga al'umma. wajibi ne kowane mutum mai riƙe da wata kujera yayi hidima ga al'ummarsa, saboda al'ummar su suka nuna bukatar ra'ayinsa kafin kaiwa ga wannan mukamin da yake tinkahu a kai.

Shin 'Rugga' da wasu 'yan kudancin ƙasar nan suke adawa da shi, sun samu kafar yin hakan ne, da rikon sakainar kashin wasu daga cikin 'yan arewa ne, don ganin suma suna adawa da shi, wani babban abun takaici ne, nayin saku-saku da wannan shirin, domin shirin shi zai taimaka matuƙa ainun wajen ganin an magance rikice-rikice wanda ya laƙume gwamman al'ummar da ba'asan iya yawansu ba, wanda kuma hakan ya samo asali ne, na yin fada tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma, inda wasu sukayi amfani da damar da suka samu suka mayar da abun ta'addanci a cikin ƙasa.

Babu shakka tun kafin zuwan turawa a ƙasar hausa,  Hausa da fulani 'yan uwan juna ne, suna zaune lafiya da junansu, har auratayya da abokanta da sauran mu'amala tana shiga tsakaninsu, da junansu. Sannan wuraren kiyo da ake cewa (burtani) kowace jiha daga cikin jihohin Najeriya akwai a cikin Arewa. kuma filayen kiyon da ake kira da sunan (burtali) yilwatacce ne, wanda hakan yasa fulani basu kaiwa ga gonakin manoma suna masu ɓarna har wanda take jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin manoman da abokaninsu makiyaya.

A lokacin da mukaji Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ambato dawowa da waɗannan wuraren kiyo ga makiyaya, munji matukar daɗi, kuma munyi sambarka da haka. Amma babban abun takaici da Allah waddai shine a lokaci guda mukaji an soke shirin saboda wata manufa ta siyasa, wanda kuma haka sam-sam ba daidai bane.

Yin adalci a tsakanin al'umma wajibi ne ba tare da nuna wariya ba ko bambanci ba, kamar yadda shi shugaban ƙasa ya dauki alƙawari a lokacin sha rantsuwar kama aikinsa, kuma yake a rubuce ga kudin tsarin mulkin ƙasar nan. Sannan wannan adaIci yana da kyau a samar da shi ga kowa, hakan zai sa samu zaman lafiya da kwanciyar hankaƙi ga kowa.

Duk da haka munyi maraba da farin ciki da wasu daga cikin gwamnatocinmu na Arewa da sunka sha alwashin aiwatar da shirin. Arewa ce tamu, muna fatan gwamnonin Arewa za su tsayu haiƙan don ganin shirin ya kankama, kuma yayi tasiri, baban burinmu shine muga kowa-da-kowa yana cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yana da kyau shuwagabannin Arewa su sanya kishin ƙasa gabansu fiye da buƙatun kansu, hakan zai taimaka wajen farfadowar Arewar da ƙimarta a idon duniya, muna fatan samun zaman lafiya kwanciyar hankali da lumana a ƙasarmu Najeriya da yankin Arewa Baki daya.

Fatan alheri ga kowa!

Wassalam

Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020