Skip to main content

Shirin tallafawa matasa na gwamnati Matawalle



Mai girma gwamnan jahar Zamfara, Hon (Dr.) Bello Mohammed Matawalle (Matawallen Maradun) ya kaddamar da shirin tallafawa matasa har su 229 marassa ayukkan yi har naira miliyan 81 a jahar Zamfara.

Bikin bude tallafin ya gudana ne a ofishin Fadama da ke Samuru Gusau.

Tallafin wanda aka baiwa matasa 229 a shirin  Fadama Wanda kacokan an bullo da shirin ne, Domin matasa Da mata da su ka Kammala karatu ba su da aikin yi Domin su dogara da kawunansu .

Mutun  229  da su ka amfana Da shirin sun fito daga kananan hukumomi 14 na jahar Zamfara. Wanda wasu za su mayar da hankali ga kiyon kaji,kiyon kifi da kuma noma.

Gwamnan ya bayyana cewa  Kudin tallafi ne ba bashi ba. An baiwa Matasan su ne, domin yin yakar zaman kashe wando ta hanyar yi kasuwanci ta yadda za su tallafi kansu har a samu cigaban tattalin arziki a jahar Zamfara.

Haka zalika gwamnan ya shawarci wadanda su ka samu wannan tallafi Da su yi amfani Da abunda su ka samu kamar yadda ya dace, domin cigaban kansu har su dauki wasu aiki.

Gwamna Matawalle ya kara Da cewa gwamnatinsa za ta cigaba Da aiki da masu son su tallafawa al'ummar jahar Zamfara ta fuskar noma da da sauran shiraruwa Da ake bullowa da su Domin taimakon Al'umma.

Yusuf Idris G
Babban Daraktan Watsa Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara.

Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
02/07/2019

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020