Zaben munistocin Shugaba Buhari
Muna fatan dogon nazarin da Shugaban kasar Najariya Muhammadu Buhari ya yi wajen zakulo munistocin da zasu tallafa masa wajen gudanar da ayyukan Kasa su kasance masu amfani ga talakawan Najeriya.
Wasu daga cikin zababbin munistocin na shugaba Muhammadu Buhari a wa'adi na farko, basu tabuka wani abun azo a gani ba, idan muka dubi irin tarin tulin matsalolin da anka ci gaba da samu daga nan zuwa cen, muna fatan a wannan Karon talakawan Najeriya za suyi dariya a kan wadannan bayin Allah da Shugaban ya zabo.
Hakika shugaba yana samun nasarar ci gaban gudanar da kowane irin aikin cigaban raya Kasa, idan har ya samu jajirtatun masu taimaka masa ta fuskoki daban-daban, a sha'anin mulki.
Muna fatan Allah ya sa wannan zabin na shugaba Buhari ya kasance alheri ga Al'ummar Najeriya baki daya.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment