Skip to main content

FADAKARWA GA MATASANMU DA KE SHIRIN RUBUTA JARABAWAR JAMB 2020!



Muna amfani da damar Domin sanar da 'yan uwa matasa Da ke Da gudurin shiga jami'a. Kamar yadda mu ka sani dole ga Dan Najeriya ya yi Jarabawar share fagen shiga jam'iya wato Jamb Kafin ya samu gurbin karatu a jami'o'in kasarmu Najeriya.

Dan haka kenan Jarabawar na da matukar muhimmanci ko ma in ce dole ce. A shekarun Da su ka wuce, ba wasu dokoki da Kai'doji da su ka bullo Da su. Sai dai kullum Kara bullo da wasu ka'idoji su ke yi da zummar ko dai inganta Jarabawar ko ba ta tsaron kaucewa Sata ko fuskantar matsalolin da ke tusgowa.

Wanda a wannan shekarar Mai kamawa sun bullo da shirin yin amfani da lambobin katin shedar Dan kasa. Ma'ana ya zama wajibi ga duk Wanda zai rubuta jamb ya kasance ya mallaki katin shedar zama Dan kasa, Domin a cikin katin lambar ta ke. A Cewar hukumar hakan ya faru ne Dan kaucewa yin rigista fiye Da daya Da wasu ke yi.

Dan haka muna amfani da wannan damar mu sanar da 'yan uwa Da uwaye duk Wanda ya San wani NASA zai zana wannan Jarabawar ya hanzarta ziyartar ofishin yin katin shedar Dan kasa mafi kusa Da shi. Domin yin rigista.

Dan Allah mu yada wannan wannan sakon Dan amfanar 'yan uwanmu! Da ba su san da wannan sabon shirin ba.
Allah ya sa mu dace amin.


Daga Sufyanu Dan iya Gummi.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...