Posts

GYARAN HAƘORI DAGA 3000 ZUWA 1000 HAR NA TSAWON MAKO DAYA.

Image
GYARAN HAƘORI DAGA 3000 ZUWA 1000 HAR NA TSAWON MAKO DAYA. A ci gaba da bukukuwan murnar sabon kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara, wanda ke gudana a yanzu haka. Ana farin cikin sanar da al'umma dake faɗin jihar Zamfara cewa; wannan cibiya mai Suna a sama, zata ci gaba da gudanar da aikin wankin haƙori kamar kyauta, domin zata karɓi Naira 1000 kacal ! Har na tsawon mako daya. Samun wannan sauƙin na zuwa ne sakamakon murnar Shiga Office Da Kwamishinan Kasuwanci da Masana'antu yayi a cikin makon nan wato (Hon Alh Yazeed Shehu Danfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamiɗon Tsafe) kuma wannan damar ta kowace, kowa na iya zuwa domin samunta matuƙar kai ɗan jihar Zamfara ne. Babban Mazaunin wannan wari ya nan a "ZAKKA PLAZ" kusa da gidan ruwa a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Maza yanzu haka ka kira waɗannan lambobin domin samu. 08064475743 08062336429 07061099637 Babban jami'i mai gudanarwa (Abdulrahman Dangon Yazeed) Muna matuƙar godiya a kan haɗin kan d...

Zuwa Ga Mai Daraja Gwamnan Jihar Zamfara a Kan Makomar Jihar

Image
Zamfara jihace wadda a cikin kasar nan idon akayi magana a kan zaman lafiya ita ce kan gaba kafin wasu jihohi, shekaru 20 da suka gaba ta, duk wani dan jihar Zamfara idon zai kwanta bacci baya rufe gidansa. Mafi yawa daga cikin gidajen al'umma a wancen lokaci bud'e suke kwana har safe, saboda zaman lafiya. A wancen lokacin komai dare mutum baya jin tsoron tashi daga wannan gari zuwa wancen, daga wannan unguwa zuwa waccen, domin baya tsaron komai.  A wancen lokacin dabbobi suna kwana a cikin daji, alhali mai su yana cikin gari hankalinsa akwance a natse! Baya tsoro wani abu.  Dukkan kasuwannin dake fadin jihar suna gudana cikin dadin rai, duk da ana kallon a wancen lokacin kamar arziki bai yilwatu ba a cikin al'umma, amma zaman lafiya ya samu, kwanciyar hankali a ko'ina. Al'umma suna gudanar da rayuwarsu irin yadda suke so, babu tsamgwama, babu hantara, ko kyara! Kaiconmu! Duk wanda ya rayu a wancen lokacin, kuma yana raye a yanzu, ya ga abin mamaki da fa...

Kira ga Hukumar Sadarwa ta kasa

Image
Kamar yadda hukumar sadarwa ta bayar da wa'adin kammala haɗe layin waya da kuma numbobin katin zama ɗan ƙasa, wanda kuma yanzu haka mutane na ci gaba da yin tururuwa wajen ofisoshin da ake yin katin na zama ɗan ƙasa, akwai bukatar hukumar dake yin wannan katin na zama ɗan kasa ta kara yilwata ofisoshin yin aikin, domin taƙaita wahala ga al'umma, wajan samun damar mallakar rijistar da milyoyin mutanen da basu samu damar yin rijistar ba suke fafutikar ganin sun samu. Dubban mutanen dake tururuwa wajen inda ake yin rijistar suna galabaita matuƙa. Wasunsu duk irin yanayin sanyin da ake fama da shi, amma a haka suke bacci a wajen, domin ganin sun mallaki katin. Wanda hakan yake janyo turmutsutsu, wasu lokutan har da faɗace-faɗace, kuma hakan yana faruwa ne sanadiyar rashin samun wadatattun wuraren da ake gudanar da aikin.  Saboda haka ya kamata wannan hukuma ta dubi yiwuwar kara wajajen gudanar da waɗannan ayyukan, domin ganin 'yan kasa waɗanda basu mallaki katin ba,...

KYAUTAR GIRMAMAWA DAGA YAZEED TRUST FUND ZUWA GA JEKADIYYAR YAZEED

Image
Shimfiɗa. Lambar yabo ta girmamawa wanda ake kira da (award) a turance wata babbar kyauta ce wadda ake bayarwa ga dukkan wanda ya shahara ta wasu fuskoki, misali; wanda ya kasance ɗan gwagwarmayar rayuwa a gefen da ya fi shahara haɗi da kwarewa, domin ƙara masa kwarin gwiwar tashi tsaye domin kara azama akan abinda yasa a gaba, domin ganin nasararsa ta ci gaba da ɗorewa har iyakar rayuwarsa. Madallah da lambar yabo ta girmamawa ga wanda ya cancanta! A 19/08/2020 gidauniyar nan mai yaɗa manufofi haɗi da yin ayyukan alheri a cikin al'umma a duk faɗin jihar Zamfara, kuma mai son ganin al'umma sun samu kowane irin sauye-sauye ta fuskar  samarwa da jama'a ingantacciyyar rayuwa, wadda ke ƙarƙashin kulawar (Alh Yazeed Shehu Dan Fulani) wanda (Comrade Rufa'i Bala UB Gusau) yake shugabanta wato; (Yazeed Trust Fund) ta karrama daya daga cikin jiga-jigan gidauniyar, wato; (Hajiya Aisheet Ibraheem, mai laƙabi da 'yar Asali'. An dubi yiwuwar, haɗi da nazarin bata wannan kyau...

Ranar Matasa Ta duniya, ina muka dosa

Image
  Shimfiɗa Kamar yadda aka saba kowace shekara majalisar dinkin duniya ta na ware 12 ga watan 8 a matsayin ranar matasa ta duniya, hakan na zuwa ne, domin nuna muhimmancin da matasa suke da shi a cikin al'umma. Salam Ko shakka babu matasa sune ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a duniya, babu wata kasa ko al'ummar ƙasar da zasu ci gaba matukar bada matasa ba, sannan ƙasa tana samun naƙasu sosai matuƙar ta mayar da matasanta saniyar ware. Idon muka kalli mafi yawa daga cikin ƙasashen duniya, musamman masu tinƙaho ta ɓangare kimiyya da ƙere-ƙere haɗi da tattalin arziki, wannan nasarar ta samo asali ne ta sanadiyar an dauki matasa da muhimmanci, an jawo su a jiki an nuna masu kowace irin kulawa, sannan aka tusa masu son ƙasa haɗi da kishinta. Najeriya tana cikin jerin ƙasashen duniya masu tinƙaho da yawan matasa, haka itace ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a ƙasashen Afrika ta yamma, sannan ita ce ƙasa mafi yawan al'ummomi mabambanta, da kuma yaruka daban-daban. Sannan t...

Yazeed Trust Fund

Image
Operation Taimakon Marayu. Jiya laraba 29/07/2020 gidauniyar Yazeed Trust Fund ta kaddamar da rabon tallafin kayan sallah wa marayu. Wannan aikin alherin da aka saba, ya gudana ne a babban ofishin kungiyar da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.  A lokacin rabon tallafin na kayan sallah, a cikin nasa bawabin shugaban gidauniyar ta Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau ya ce, sun yi wannan nazarin ne  la'akari da muhimmancin haka, kasancewar marayu basu da wani galihu, ya kamata su ma a in ganta rayuwarsu a ranar sallah su fito kamar kowa. Taimakon marayu da marasa galihu a cikin al'umma abu ne da ba sabon ba, domin aikin ne wanda ya kasance kamar jini a cikin jikin (Alh Yazeed Shehu Danfulani mai Doya, Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe) bayar da wannan tallafin ya samu halartar manyan mutane da dama daga cikin har da iyaye mata, da sauran al'umma, wadanda suka shedi wannan aikin alheri. Haka shugaban kwamitin bayar da wannan t...

Sabunta Riyoji a Cikin Gusau!

Image
A yau ne Assabar 18/07/2020 Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta gudanar da gyaran wasu riyojin fanfuna a filin na yawo dake shiyar Sabon fege a Cikin gundumar Galadima a karamar Hukumar Gusau ta jihar Zamfara. Gyaran na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke matukar neman bukatar taimako musamman abunda ya shafi bangaren samar da ruwan sha masu tsafta. A ci gaba da rangadin bayar da kowane irin taimako hadi da bada gudunmuwa a cikin al'umma, tawagar Gidauniyar Yazeed tayi kicibus da wasu riyoji da ake ci gaba da ibar ruwa a ciki, duk da kasancewar akwai kwatoci da sauran wasu ledodi da kayan kazanta. Kai tsaye jakadun Alh Yazeed Shehu Danfulani karkashin jagorancinsa, ta hannun shugaban amintattun gudanarwa na tafiyar, kuma shugaban kungiyar Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau, suka dukufa ka'in da Na'in wajan gyaran riyojin, domin sabuntasu hadi da mayar da su sabbi, ta hanyar saka masu Tayis da kuma yi masu aiki na zamani, domin samar da ruwa masu ts...