Skip to main content

Ranar Matasa Ta duniya, ina muka dosa

 


Shimfiɗa


Kamar yadda aka saba kowace shekara majalisar dinkin duniya ta na ware 12 ga watan 8 a matsayin ranar matasa ta duniya, hakan na zuwa ne, domin nuna muhimmancin da matasa suke da shi a cikin al'umma.


Salam


Ko shakka babu matasa sune ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a duniya, babu wata kasa ko al'ummar ƙasar da zasu ci gaba matukar bada matasa ba, sannan ƙasa tana samun naƙasu sosai matuƙar ta mayar da matasanta saniyar ware. Idon muka kalli mafi yawa daga cikin ƙasashen duniya, musamman masu tinƙaho ta ɓangare kimiyya da ƙere-ƙere haɗi da tattalin arziki, wannan nasarar ta samo asali ne ta sanadiyar an dauki matasa da muhimmanci, an jawo su a jiki an nuna masu kowace irin kulawa, sannan aka tusa masu son ƙasa haɗi da kishinta.



Najeriya tana cikin jerin ƙasashen duniya masu tinƙaho da yawan matasa, haka itace ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a ƙasashen Afrika ta yamma, sannan ita ce ƙasa mafi yawan al'ummomi mabambanta, da kuma yaruka daban-daban. Sannan tana cikin ƙasashen duniya masu ƙarfin faɗa a ji a duniya, sannan ita ce ƙasa wadda mafi yawa daga cikin mutanenta bakar fata ne, masu jurewa kowace irin gwagwarmaya ta yau da kullum, sannan tana cikin ƙasashen da ke da tarin addinai da dama mabambanta.


Idan muka kalli wasu daga cikin jerin ƙasashen duniya da suka ci gaba, musamman a yankin turai, duk da kasancewar ƙasashen mutanensu waɗanda ko a junansu basu cika yadda da su ba, to amma duk da haka suna samun gagarumin haɗin kai wajan gina ƙasa haɗi da cigabanta. Wannan ya sa sun ka baiwa matasansu fifiko wajan gudanar da wasu ayyuka musamman abubuwan da suka shafi yin nazari da himmatuwa wajan bincike akan laluɓo hanyoyin kawo sauye-sauye a cikin ƙasashensu, wanda hakan ya basu damar riƙe kambun ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, da kuma yiwa sauran ƙasashe zarra wajan samar da kayan ci gaban ƙasa. Misali; kamar manyan wayoyin hannu, na'urori masu aiki da kwakwalwa, da dangoginsu.



Idan muka yi nazari a tsanake, zamu daɗe muna dasa ayar tambaya akan to wai me yasa mu a Afrika har yanzu mun ka kasa ta ɓangaren irin wannan ci gaba. Bari mu dawo Ƙasarmu ta gado. A Najeriya akwai ɗinbin Matasa waɗanda Allah ya baiwa fasaha ta ɓangarori da dama, wanda wasu daga ciki sun kware wajan iya zane, wasu sun kware a ɓangare iya sarrafa ƙarafa, waɗansu  sun kware a ɓangare injiniyanci, wasu kuma sun kware ta fuskar samar da abubuwan more rayuwa da dai wasu fannoni masu matuƙar yawa. To amma ina gizo yake saƙar? Ta wannan sashen kam sai mu dora alhakin wannan ga shugabanni, domin su suke da alhakin bincike haɗi da zaƙulo masu baiwa ta taimakawa ƙasa, domin ƙarfafa musu gwiwa ta kowane fanni, domin ganin an bunƙasa ƙasa ta kowane hauji.



Babu maraya sai raggo! Ko shakka babu a matsayinmu na matasa masu tasowa, bai kamata mu matsaya ci ma kwance ba, ya zama wajibi mu tsayu da kafafunmu wajan dogaro da kanmu domin biyan buƙatun kanmu, baya zama dalili ga matashi ya ce tun da yayi karatu mai nisan zango, ya zauna sai ya samu aikin yi daga wajan gwamnati ba, kasancewar matuƙar dambu ya yawa bayajin mai, ya kamata matashi ya sa a ransa idon yayi karatu yayi ne domin kariyar mutuncin shi, ba don ya samu aiki daga wajan gwamnati ba, mu daina raina sana'a komai ƙanƙantarta domin bamu san inda arziƙinmu ya ke ba, mu tashi kawai mu fantsama wajan nema, insha Allahu da sannu wata rana zamuyi gamdakatar.



Ba ya zama dalili, a matsayinmu na matasa muyi nazarin daukar makamai muna tare hanyoyi, garuruwa, da ƙauyuka muna ansar dukiyoyin 'yan uwanmu, domin wannan baya zama cikin jerin aikin mazantaka, matashi jajirtacce shine wanda ke gwagwarmayar neman halal cikin kowane yanayi, saboda haka ya na da kyau mu chanza tunane daga marar kyau zuwa wanda ya dace, hakan zai sa mu gina rayuwa mai inganci wadda bata da fargaba.


Kowa a cikin ƙasar nan akwai irin gudunmuwar da zai iya bayarwa wajan gina ta haɗi da ci gabanta, mu dai kasance kawai jekadu na gari a duk inda mun ka tsintsi kanmu, mu kasance masu gaskiya da riƙon Amana, masu alkawari da kuma kaucewa cin amana, hakan zai taimaka mana wajan gina kanmu da kuma ƙasarmu.


Babu wata ƙasa da zata ci gaba matukar al'ummarta basu da haɗin kai, domin sai an samu haɗin kai da kaunar juna sannan za a samu dukkan ci gaban da ake buƙata. Ina addu'ar Allah ya kawo mana lafiya da zama lafiya a Najeriya da Afrika dama duniya baki daya.


Barka da ranar Matasa ta Duniya


Happy International Youths Day



Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau Shugaban Ƙungiyar Matasa 'Yan Gwagwarmaya ta Ƙasa da Ƙasa. 08133376020

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020