Zuwa Ga Mai Daraja Gwamnan Jihar Zamfara a Kan Makomar Jihar
Zamfara jihace wadda a cikin kasar nan idon akayi magana a kan zaman lafiya ita ce kan gaba kafin wasu jihohi, shekaru 20 da suka gaba ta, duk wani dan jihar Zamfara idon zai kwanta bacci baya rufe gidansa. Mafi yawa daga cikin gidajen al'umma a wancen lokaci bud'e suke kwana har safe, saboda zaman lafiya. A wancen lokacin komai dare mutum baya jin tsoron tashi daga wannan gari zuwa wancen, daga wannan unguwa zuwa waccen, domin baya tsaron komai.
A wancen lokacin dabbobi suna kwana a cikin daji, alhali mai su yana cikin gari hankalinsa akwance a natse! Baya tsoro wani abu.
Dukkan kasuwannin dake fadin jihar suna gudana cikin dadin rai, duk da ana kallon a wancen lokacin kamar arziki bai yilwatu ba a cikin al'umma, amma zaman lafiya ya samu, kwanciyar hankali a ko'ina. Al'umma suna gudanar da rayuwarsu irin yadda suke so, babu tsamgwama, babu hantara, ko kyara!
Kaiconmu!
Duk wanda ya rayu a wancen lokacin, kuma yana raye a yanzu, ya ga abin mamaki da fargaba. Ganin irin yadda komai ya tab'arb'are dole ya zubar da hawaye, domin ko a cikin bacci dan Zamfara bai tab'a yin mafarkin zai samu kansa a cikin wannan yanayi ba.
Sanadiyar matsalar tsaro dake damunmu a jihar Zamfara, komai ya lalace. Kasancewar babu yadda za'ayi a samu arziki da salama babu zaman lafiya. Zaman lafiya shine kashin bayan ci gaba kowace al'umma a rayuwa.
Yanzu kauyuka da birane babu yadda a tsakaninsu, al'ummomi babu yadda. Ba a ga-maciji tsakanin manoma da Fulani makiyaya. Akwai tada hankali idan ana lissafa dubban mutanen da sunka rasa rayukansu hadi da cilastawa dubban wasu jama'ar barin muhallansu, kuma milyoyin nairori da anka tafka asara sakamakon wannan mumman tashin hankali basu lissafuwa.
Babu shakka lokaci yayi da ya kamata a cire siyasa, a tashi tsaye kai da fata, wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Babban burin talaka duk baifi a samar masa da zaman lafiya ba, a baiwa 'ya'yansa ilimi, a samar masa da ruwan sha, da hanyoyi da kuma kula da lafiyarsa, amma wannan ya gagara. Kaicon talaka a yau!
Idon gari babu al'umma, ta yaya za'a samu jagora? Idon gari babu jama'a ta yaya za'a samu jin dadin shugabanci? Idon babu zaman lafiya ta yaya za a samu arziki ? Duk lokacin da al'umma sun ka kasance cikin fargaba da tashin hankali, to babu yadda za'ayi komai ya daidaita.
A bisa wannan nake kira ga shugabannimu a mataki daban-daban da cewa ya kamata suji tsoron Allah, kuma su san komai dadewa inda rayuwar talaka ta tafi, suma komai dadewa dole su bakunci wajen, kuma Allah ya nan madakata. Ya kamata su dawo cikin haiyacinsu, su hada kansu, su tsaya da murya daya, a matsayin tsintsinya madauri daya domin su kawo mana karshe wannan tashin hankali.
Wallahi wallahi al'umma suna cikin tashin hankali da fargaba, musamman mazauna kauyuka, wallahi basu iya bacci idon dare yayi , wasun su a daji suke bacci saman bishiyoyi.
Muna kira da babbar murya da a daina sanya siyasa a cikin harkar tsaro, domin sanya siyasa a ciki baya kaiwa ga nasara. Al'ummarmu suna bukatar agaji. A taimaka don Girman Allah!
Ya ubangiji muna rokonka da sunayenka masu tsarki, da suffofinka madaukaka, ya Allah ka kawo mana zaman lafiya da aminci a jiharmu ta Zamfara, Arewa da Najeriya baki daya. Ya Allah ba don halinmu ba. Ka zama gatanmu.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau
Comments
Post a Comment