KYAUTAR GIRMAMAWA DAGA YAZEED TRUST FUND ZUWA GA JEKADIYYAR YAZEED



Shimfiɗa.


Lambar yabo ta girmamawa wanda ake kira da (award) a turance wata babbar kyauta ce wadda ake bayarwa ga dukkan wanda ya shahara ta wasu fuskoki, misali; wanda ya kasance ɗan gwagwarmayar rayuwa a gefen da ya fi shahara haɗi da kwarewa, domin ƙara masa kwarin gwiwar tashi tsaye domin kara azama akan abinda yasa a gaba, domin ganin nasararsa ta ci gaba da ɗorewa har iyakar rayuwarsa. Madallah da lambar yabo ta girmamawa ga wanda ya cancanta!


A 19/08/2020 gidauniyar nan mai yaɗa manufofi haɗi da yin ayyukan alheri a cikin al'umma a duk faɗin jihar Zamfara, kuma mai son ganin al'umma sun samu kowane irin sauye-sauye ta fuskar  samarwa da jama'a ingantacciyyar rayuwa, wadda ke ƙarƙashin kulawar (Alh Yazeed Shehu Dan Fulani) wanda (Comrade Rufa'i Bala UB Gusau) yake shugabanta wato; (Yazeed Trust Fund) ta karrama daya daga cikin jiga-jigan gidauniyar, wato; (Hajiya Aisheet Ibraheem, mai laƙabi da 'yar Asali'.


An dubi yiwuwar, haɗi da nazarin bata wannan kyautar ne la'akari da irin ƙoƙarin da ta ke bayarwa wajan ci gaban tafiyar (Alh Yazeed Shehu Dan Fulani Mai Doya Garkuwan Matasan Gusau, Lamiɗon Tsafe). An yi hakan ne domin ƙara mata karsashi haɗi da kwarin gwiwar tsayuwar tsayin daka wajan fafutikar ci gaban al'umma ta kowane fanni. 



Dukkan masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar gidauniyar Yazeed Trust Fund ne suka aminta da wannan kuduri, haka a lokacin da bikin bayar da wannan kyautar ke gudana, an kara karrama ta da kyautar Jakadiyar Yazeed, la'akari da cancantarta na rike wannan kambu, muna fatan hakan zai zama silar kara tsayuwa a cikin wannan tafiya.


Wasu daga cikin kungiyoyin fafutika da dama sun samu damar halartar wannan taro, da muhimman mutane da dama, a lunguna da sakunan jihar Zamfara da wasu daga cikin maƙotan jihar Zamfarar. Da dukkan takwarorinta mata da suka halarci wajan domin taya murna haɗi da shedar da bada wannan kyautar.


Jekadiyyar Yazeed ɗin a nata jawabi ta bayyana farin cikinta marar bisaltuwa haɗi da rera wasu baituka na yabo ga fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S.A.W), kasancewarta fasihiyar mawaƙiya wadda ke isar da saƙonni cikin hikima.


'yar Asalin, kuma. Tayi addu'ar Allah ya maida kowa gida lafiya, haɗi da addu'ar Allah ya bar zumunci. Kuma ya kara basu hakurin haɗin kai domin aiki tare wajan ciyar da jiha dama ƙasa baki daya a gaba.


Taron wanda ya gudana a Nafes (NFirst Hotel) a kan titin shiyar Samaru a tudun wada Ƙaramar Hukumar Gusau a jihar Zamfara, ya gudana kuma ya kammala lafiya.


Allah ya taimaki Jakadiyyar Yazeed.


Allah ya taimaki Alh Yazeed Shehu Danfulani


Allah ya taimaki Yazeed Trust Fund


Allah ya taimaki shugabanni da membobin Yazeed Trust Fund


Allah ya taimaki Gusau da Jihar

  Zamfara da Najeriya baki daya..



Rahoto


(Mai Apple).


Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’