Kira ga Hukumar Sadarwa ta kasa
Kamar yadda hukumar sadarwa ta bayar da wa'adin kammala haɗe layin waya da kuma numbobin katin zama ɗan ƙasa, wanda kuma yanzu haka mutane na ci gaba da yin tururuwa wajen ofisoshin da ake yin katin na zama ɗan ƙasa, akwai bukatar hukumar dake yin wannan katin na zama ɗan kasa ta kara yilwata ofisoshin yin aikin, domin taƙaita wahala ga al'umma, wajan samun damar mallakar rijistar da milyoyin mutanen da basu samu damar yin rijistar ba suke fafutikar ganin sun samu.
Dubban mutanen dake tururuwa wajen inda ake yin rijistar suna galabaita matuƙa. Wasunsu duk irin yanayin sanyin da ake fama da shi, amma a haka suke bacci a wajen, domin ganin sun mallaki katin. Wanda hakan yake janyo turmutsutsu, wasu lokutan har da faɗace-faɗace, kuma hakan yana faruwa ne sanadiyar rashin samun wadatattun wuraren da ake gudanar da aikin.
Saboda haka ya kamata wannan hukuma ta dubi yiwuwar kara wajajen gudanar da waɗannan ayyukan, domin ganin 'yan kasa waɗanda basu mallaki katin ba, sun samu damar yinsa ba tare da shan wahala sosai ba. Duk da munsan hukumar tayi namijin ƙoƙari na irin tsawon lokacin da ta dauka tana gudanar da wannan aiki a cikin ƙasa.
Ko ba komai haɗewar layin waya (Sim Card) da kuma katin zama ɗan ƙasa( NIN) yana da matuƙar muhimmancin gaske, domin dukkansu abubuwa ne da suke tattare da dukkan bayanai na mutum, wanda kuma idon aka samu nasarar wannan aiki, hakan zai taimaka wajen samar da tsaro a cikin kasa, domin duk wanda ya san akwai bayanansa a hukumance da wahala ya aikata wani babban laifin da zaisa farautarsa.
Muna fatan Allah ya kawo mana zaman lafiya madauwami a Najeriya, ya bamu haɗin kai da kaunar juna. Ya karo mana arziki mai albarka.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment