Skip to main content

Posts

_KUNGIYAR MURYAR TALAKA ZA TA KARRAMA GWARZAYEN SHEKARA:_*

Duk Shekarar Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara ta kan zabi wasu Muhimman mutane Tana KARRAMA su. , akan wasu Muhimman gudunmuwowi da sunka bayar wajen cigaban al'umma a bangarensu! A lokacin Babban taron kungiyar na Shekara-shekara. Sai dai a wannan Shekarar shirin zai dan sauya sabon salo. A wannan Shekarar za mu Kalli jagororinmu ne, tun daga Kansiloli, shuwagabannin kananan hukumomi, 'yan Majalissar Dokokin na jaha, 'Yan Majalissar wakilai na tarayya da kuma 'yan Majalissar dattawa na tarayyarmu. Inda kowane bangare cikinsu za ku zabi daya da ya zama zakara wajen kyautatawa al'ummarsa, mu kuma mu karrama shi. Haka zalika za mu zabo wasu Muhimman mutane zuwa biyar da za mu fitar cikinsu ku zabi daya, a matsayin gwarzon SHEKARA. Ga ranakun da zaben zai Gudana. 1.kansiloli 1/1/2018 to 3/1/2018 2.ciyamomi 4/1/2018 to 6/1/2018 3. State House Assembly  7/1/2018 to 9/1/2018 4.National Assembly 10/1/2018 to 12/1/2018 5.Senators 13/1/2018 t...

Za A Sake Kakaba Ma Koriya Ta Arewa Takunkumi Mai Tsanani

A cigaba da sa kafar wando guda da Amurka da Koriya Ta Arewa ke yi, saboda cigaba da shirin nukiliya da Koriya Ta Arewa ke yi, Majalisar Dinkin Duniya, bisa bukatar Amurka, za ta kakaba ma Koriya Ta Arewa wani sabon takunkumin da zai sa samun man fetur ya ma ta wahala. Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya zai kada wata kuri’a kan wani rukuni na takunkumi, da zummar dada tsaurin hanyoyin da Koriya Ta Arewa ta ke bi wajen sayo mai daga kasashen waje, wanda ke taimaka mata wajen haramtaccen shirinta na nukiliya. Wannan takunkumin da ke tafe martani ne ga kaddamar da wani sabon makami mai linzami mai iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata da Koriya Ta Arewa ta yi ran 28 ga watan Nuwamba, wanda ta yi wa lakabi da Hwasong-15, wanda ta ce na iya jefa makamin nukiliya a ko ina a Amurka. Wannan shi ne karo na uku da Koriya Ta Arewa ta kaddamar da makami mai linzami mai iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata a 2017; kuma shi ne karo na 20 da ta kaddamar da makami mai linzami a sheka...

Jami’An Yansanda Sun Yi Caraf Da Wasu Yan Fashi Da Makami Su 23

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu fitinannun yan fashi da makami guda 23 dake tare mutane a kan hanyar Abuja-Kaduna-Suleja har zuwa Minna. Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace miyagun mutanen sukan hada da satar mutane, tare da amsan kudaden fansa. Yansanda sun tabbatar da kama ya fashin da bindigu, alburusai, wukake, kaho, katunan banki da kuma shanun mutane da dama. Majiyar  ta ruwaito rundunar Yansandan jihar Kaduna ta samu nasarar kama wasu samari guda biyu da suka shahara wajen satar mutane a jihar Kaduna, Adamu Lawan, da Aminu Lawan. Ayyukan masu garkuwa da mutane na cigaba da ta’azzara a jihar Kaduna a yan kwanakin nan, inda miyagun mutanen ke amfani da sabbin salon satar mutane, don a yanzu har almajirai basu bari ba.

Jam’Iyyun Adawar Najeriya Na Kokarin Yiwa APC Taron-Dangi

Mun ji cewa wata Jam’iyya a Najeriya mai suna PPP na shirin doke Jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019. Jam’iyyar tace amma fa kifar da Gwamnati mai ci a Kasar sai an yi da gaske. Jam’iyyar PPP tuni ta fara hangen zaben 2019 inda tace za ta nemi goyon bayan sauran Jam’iyyun adawa na kasar da su yi taron-gwiwa domin yin waje da APC. Kamar yadda mu ka samu labari Shugaban Jam’yyar ya bayyana wannan. Damian Ogbonna wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar na PPP na kasa yace babu Jam’iyyar da ta isa ta kada Gwamnati mai ci ita kadai . Don haka ne yace dole ayi kokarin hada karfi-da-karfe domin ganin an iya doke Jam’iyyar da ke mulki 2019. Jam’iyyar ta na kokarin tuntubar sauran Jam’iyyun adawan kasar irin su PRP da CAA domin ganin an ba APC kashi. Ogbonna ya kuma nemi Jama’a su yi kokarin fita zabe mai zuwa domin ko da yana ganin har yanzu ana tafka magudin zabe.

Hare-Haren Saudiyya Ya Kashe Mutane136 A Kasar Yaman – UN

Majalissar Dinkin Duniya (UN) ta ce hare-haren da kasar Saudiyya da kawayenta su ka kai wa kasar Yaman a cikin kwanaki goma yayi sanadiyar mutuwar fararen hula 136. Kakakin kungiyar kare hakkin dan Adam dake karkarshin Majalissar Dinkin Duniy, Rupert Colville, ya bayyana haka a lokacin da yake zanatwa da manema labaru a Geneva. Rupert Colville ya nuna damuwar sa akan sammamen da sojojin Saudiya da kawayenta suke kai wa sojojin yan tawayen kabilar Houthi a Yaman inda suka kashe mutane 136. Hare-haren Saudiyya ya kashe yan Yaman Daya daga cikin wuraren da suka kai sumame, har da gidan yarin Sana’a inda mutane 45 suka mutu. KU KARANTA : Yan tawayen kabilar Houthi sun sake kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami A cikin wannan makon ne yan tawayen kabilar houthi suka harba wa birnin Riyadh dake kasar Saudiya makami mai linzami . Amma gamayyar kugiyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta wajen yakar yan tawayen kabilar Houthi sun ce sun samu nasarar tare makami mai linzami ...

Gwamnatin Tarayya Ta Bawa David Mark Wa’Adin Kwanaki 21 Ya Tattara Nasa-Ya-Nasa Ya Fice Daga Gidan Shugaban Majalisar Dattijai

Gwamnatin tarayya ta zargi tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark, da mallakar gidan shugaban majalisar ta haramtacciyar hanya. Kwamitin bincike da kwato kadarorin gwamnatin tarayya da ofishin shugaban kasa ya kafa a watan Satumba karkashin jagorancin Cif Okoi Obono-Obla ya gano hakan kuma ya dibawa Mark wa’adin kwanaki 21 ya tattara nasa ya nasa ya bar gidan. Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai David Mark A cikin takardar wa’adin kwanakin barin gidan da kwamitin ya aikewa Mark, an bukaci da ya gabatar da wata hujja, idan yana da ita, da zata hana gwamnati fitar da shi daga gidan. Saidai David Mark ya garzaya babban kotun tarayya dake Abuja domin dakatar da gwamnatin daga fitar da shi daga gidan da kuma kwace mallakin gidan daga hannun sa. DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa wani maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki Har yanzu kotun bata saurari karar da Mark ya shigar gaban na ta ba. Gidan shugaban majalisar dattijai dake kan ...

An Sake Kaiwa Saudiyya Hari Da Makami Mai Linzami

Gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake yi da ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen ta ce ta tare wani makami mai linzami da aka harba birnin Riyadh, in ji kafafen watsa labaran Saudiyya. Ganau a babban birnin kasar Saudiyya sun wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya kuma an ba da rahotannin rushewar wurare. Gidan talabijin din al-Masirah na ‘yan tawayen Houthi ya bayar da rahoton da ke cewa mayakan kungiyar sun harba makami mai linzami samfurin Burkan-2 kan fadar Yamama. Ayatollah Khamenei na Iran ‘Hitler’ ne – Yariman Saudiyya An yi barazanar kai wa Saudiyya hari Wani makami mai linzami da ‘yan tawayen suka harba a watan jiya ya kusa fada wa kan filin jirgin saman Riyadh. Saudiyya da Amurka sun zargi Iran da bai wa ‘yan tawayen Houthi makamai masu linzami. Iran ta musanta zargin. Tun a shekarar 2015 ‘yan tawayen ke yakar gwamnatin Yemen da kuma gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta.