Posts

Showing posts from April, 2018

GODIYA TA MUSAMMAN GA MASARAUTAR GUSAU A KAN AMINCEWA DA BADA SARAUTAR JARUMIN GUSAU GA ANAS HAMISU ANALYS!

Image
Daga; Nura Muhammad Mai Apples Gusau ------------------------------¥----------------------------- Hakika muna mika godiyar mu Ga Allah Madaukakin Sarki Mai kowa mai Komai Wanda Cikin ikonsa ya Nufa Anka Baiwa Mai Gidanmu Sarautar (JARUMIN GUSAU) Gaskiya babu ko Kokontu wannan Sarautar ta dace da shi, kuma ta cencenceshi, kasancewarsa Mutum mai Biyayya haziki kuma gwazo. Hon, Anas Hamisu Analyst Jarumin Gusau. muna matukar murna da alfahari da wannan Sarautar ta JARUMIN GUSAU da anka  baiwa Wannan bawan Allah, Anas Hamisu Analyst JARUMIN GUSAU ya kasance abin ko'i ga Al'umma Wajan bada gudun muwa ta kowane fanni domin ci gaban al'ummar Gusau da kewayenta, yunkurinsa wajan bada tallafi ga matasa da kyakkyawar manufofinsa na Alkhairi.  Mai Alfarma Sarkin katsinan Gusau Dr. Ibrahim Bello Sardaunan konaka, muna Addu'ar Allah ya dafa  maka ga duk kanin al'amurranka kuma ya baka nasara akan mulkin ka ya daukaka Masarautar Gusau da masu son ci gabanta, A gefe...

BABBAN TARON KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA KASA RESHEN JIHAR ZAMFARA KARO NA UKKU YA 'KAYATAR!

Image
Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau  Kasancewar kungiyar muryar talaka ta Kasa reshen jihar Zamfara kusan itace uwa mabada mama ga takwarorinta na wasu jihohin kasar nan, jiya Lahadi 15/04/2018 Tayi babban taronta Wanda ta Saba Duk shekara Wanda Wannan Karon shine karo  na ukku, a cikin jerin kwanon shiraruwanta Wanda ta Saba Yi, Hakika Wannan Karon kusan zamu iya cewa ya samu Gagarumin nasara. Irin yadda mun kaga shirin ya samu tsari mai kyau, ta hanyar yadda Anka rarraba membobin kungiyar kowane da nashi aiki, mutane da dama sun sauki darasi a cikin bayanan manyan Malamai, kamarsu Dr, Murtala Kaura, da Prof, Jibiya, ko shakka babu irin yadda sunka gabatar da bayanai wajan Abin sai dai Sam Barka. Hakika 'YA'yan kungiyar muryar talaka reshen jihar Zamfara sun Nuna dattako matuka ainun, irin yadda sunka bada hadin Kai, ankayi Wannan babban Taron lafiya kuma munka kammala lafiya, Duk da wasu daga ciki, sunsu su bata tsarin ta hanyar yin kutse GA ayukan da ba...

MADARASATUL DARUL TAUHEED WAL-HADITH, FONFON AMMANI, SHIYAR UNGUWAR TOKA GUSAU TAYI WALIMAR SAUKAR DALIBAI 60

Image
Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau. Wannan shahararriyar makarantar mai suna a sama, wadda ta kware wajan koyar da ilimin yara tsintsa! ilimin gyara lahirarsu wato addinin musulunci yau asabar 20/07/1439hijira, Wanda yayi dai-dai da Asabar 07/04/2018miladiya. Ta samu nasarar saukar da Dalibai su Sittin. Hakika Wannan wani babban ci gaba ne Wanda addinin musulunci YA samu, walimar ta samu dandazon mahalarta a ko'ina a cikin Gusau babban birnin na jihar Zamfara, da sassa daban-daban dake lunguna da sakunan Wannan jihar, Malaman Wannan shahararriyar makarantar Sun Nuna kwazon su haikan wajan maida hankali a kan abinda ya shafi koyar da ilimin   addinin musulunci, Da Wannan muke Kira da babbar murya ga Gwamnatin jihar Zamfara da tadubi Wannan shahararriyar makarantar wajan taimaka musu da Karin ajujuwa na Musamman domin Kara basu Kwarin gwiwar fadada koyarwar da suke. ''Kasancewar Wannan makarantar tana matukar bukatar fadadawa Kasancewar ta karama, ...

Mutum ya hadiye burushin da yake wanke baki da shi

Image
Mutum ya hadiye burushin da yake wanke baki da shi Likitoci a kasar Kenya sun yi nasarar cire burushin wanke baki daga cikin wani mutum bayan da ya hadiye shi. David Charo ya ce ya hadiye burushin ne bisa kuskure ranar Lahadi, lokacin da yake wanke bakinsa. Ya shafe kwana biyar yana yawo tsakanin asibitocin yankin a kokarin da yake ne neman magani. Yawancin asibitocin sun ki karbarsa suna masu cewa ba su da kwarewar da za su iya yi masa tiyata. Bayan da abin ya ci tura ne aka mika shi ga Dokta Ramadhan Omar a wani asibiti mai zaman kansa, wanda ya yi nasarar yi mata tiyata.  captionBurushin ya shafe kwana shida a cikin David Charo Hoton wurin da aka dauka ya nuna yadda burushin ya makale a cikin Mista Charo. Jama'a da dama sun nuna dimuwa kan labarin a shafukan sada zumunta. Rahatanni sun ce a yanzu Mista Charo na ci gaba da murmurewa a asibitin da ke birnin Mombasa. Wadansu bayanai sun nuna cewa ya shafe shekara 20 yana amfani da shi. Nura Muhammad Mai App...

Oyo: An Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Fyade

Image
Gangamin adawa da aikata fyade Gwamnatin jihar Oyo ta yi gargadi tare da shan alwashin hukunta duk wani mutum da aka kama da laifin yin fyade a jihar. Da yake tabbatar da wannan gargadi mataimakin gwamnan jihar Oyo, Moses Alake Adeyemo, yayi gargadin cewa duk wani mutum da aka kama da laifin yin fyade komai girman mukaminsa a kai rahotansa ga ‘yan sanda, don tabbatar da ganin doka ta yi aikinta. Haka kuma mataimakin gwamnan ya bukaci mata a jihar da su rinka saka mai kyau don kaucewa jan hankalin masu yin fyade. Hukuncin duk wani da aka kama da laifin yin fyade a jihar Oyo shine ‘daurin shekaru 14 a gidan kaso, shi kuma wanda aka kama da laifin lalata kananan yara zai fuskanci ‘daurin rai da rai. A baya dai hukumar kididdiga ta kasa ta nuna cewa babban birnin tarayya Abuja da Legas sune aka fi samun rahotannin fyade masu yawa a Najeriya inda suke da alkaluma 58,566 kuma a jihar Legas aka fi samun fyade a shekarar 2016. A yayin da jihohin Katsina da Abia ke da karancin f...

MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. ZA TA YI GAGARUMIN BIKIN BAYAR DA TALLAFI GA MATA DA MATASA.

Image
_* A madadin wannan Kungiyar Muryar Talaka Reshen jahar Zamfara, Na gayyatarka/ki zuwa wajen gagarumin taron da Kungiyar ke yi a duk Shekara. A gun Taron za mu da bayar da tallafin na Injinonin nikan taliya da fulawar za su Fara aiki da ita, kayan aski, da kuma kayan wanki da gyaran talkami ga matasa ga mutun hamsin tare da kaddamar gagarumin shirinmu na tallafawa matasa su dogara da kansu (Muryar Talaka Empowerment Support 2018) ta hanyar koyar da su sana'o'in hannu tare da ba su kayan aiki, kyauta. Haka zalika za a wannan taron za mu karrama Wasu jajirtattun shuwagabanninmu na jahar Zamfara da sunka ciri tuta, a wajen yiwa Al'ummarsu abubuwan azo a gani. Sai kuma Gabatar da Kasida mai taken "Muhimmancin koyon Sana'o'in hannu ga Matasa" Bikin zai gudana ne, Kamar haka; Wuri: Jb Sakateriya, Gusau Rana: 15-4-2018 Lokaci: 10:00 Sanarwa: Mashkur A Alkali Tsafe (Member a kwamitin Watsa Labarai na wannan bikin.)