MADARASATUL DARUL TAUHEED WAL-HADITH, FONFON AMMANI, SHIYAR UNGUWAR TOKA GUSAU TAYI WALIMAR SAUKAR DALIBAI 60
Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.
Wannan shahararriyar makarantar mai suna a sama, wadda ta kware wajan koyar da ilimin yara tsintsa! ilimin gyara lahirarsu wato addinin musulunci yau asabar 20/07/1439hijira, Wanda yayi dai-dai da Asabar 07/04/2018miladiya. Ta samu nasarar saukar da Dalibai su Sittin.
Hakika Wannan wani babban ci gaba ne Wanda addinin musulunci YA samu, walimar ta samu dandazon mahalarta a ko'ina a cikin Gusau babban birnin na jihar Zamfara, da sassa daban-daban dake lunguna da sakunan Wannan jihar,
Malaman Wannan shahararriyar makarantar Sun Nuna kwazon su haikan wajan maida hankali a kan abinda ya shafi koyar da ilimin addinin musulunci,
Da Wannan muke Kira da babbar murya ga Gwamnatin jihar Zamfara da tadubi Wannan shahararriyar makarantar wajan taimaka musu da Karin ajujuwa na Musamman domin Kara basu Kwarin gwiwar fadada koyarwar da suke.
''Kasancewar Wannan makarantar tana matukar bukatar fadadawa Kasancewar ta karama, haka muna amfani da Wannan damar wajan Taya wadannan yara murnar sauke Al'Qur'ani mai tsarki, da fatan zasuyi aiki da abinda sunka koya a cikin alkur'anin mai tsarki, kuma da fatan musulunci zaiyi Alfahari dasu.
Rahoto na Musamman, Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau
Comments
Post a Comment