Mutum ya hadiye burushin da yake wanke baki da shi

Likitoci a kasar Kenya sun yi nasarar cire burushin wanke baki daga cikin wani mutum bayan da ya hadiye shi.
David Charo ya ce ya hadiye burushin ne bisa kuskure ranar Lahadi, lokacin da yake wanke bakinsa.
Ya shafe kwana biyar yana yawo tsakanin asibitocin yankin a kokarin da yake ne neman magani.
Yawancin asibitocin sun ki karbarsa suna masu cewa ba su da kwarewar da za su iya yi masa tiyata.
Bayan da abin ya ci tura ne aka mika shi ga Dokta Ramadhan Omar a wani asibiti mai zaman kansa, wanda ya yi nasarar yi mata tiyata.
captionBurushin ya shafe kwana shida a cikin David Charo
Hoton wurin da aka dauka ya nuna yadda burushin ya makale a cikin Mista Charo.
Jama'a da dama sun nuna dimuwa kan labarin a shafukan sada zumunta.
Rahatanni sun ce a yanzu Mista Charo na ci gaba da murmurewa a asibitin da ke birnin Mombasa.
Wadansu bayanai sun nuna cewa ya shafe shekara 20 yana amfani da shi.
Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Comments
Post a Comment