MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. ZA TA YI GAGARUMIN BIKIN BAYAR DA TALLAFI GA MATA DA MATASA.


_*

A madadin wannan Kungiyar Muryar Talaka Reshen jahar Zamfara, Na gayyatarka/ki zuwa wajen gagarumin taron da Kungiyar ke yi a duk Shekara.

A gun Taron za mu da bayar da tallafin na Injinonin nikan taliya da fulawar za su Fara aiki da ita, kayan aski, da kuma kayan wanki da gyaran talkami ga matasa ga mutun hamsin tare da kaddamar gagarumin shirinmu na tallafawa matasa su dogara da kansu (Muryar Talaka Empowerment Support 2018) ta hanyar koyar da su sana'o'in hannu tare da ba su kayan aiki, kyauta.

Haka zalika za a wannan taron za mu karrama Wasu jajirtattun shuwagabanninmu na jahar Zamfara da sunka ciri tuta, a wajen yiwa Al'ummarsu abubuwan azo a gani.

Sai kuma Gabatar da Kasida mai taken "Muhimmancin koyon Sana'o'in hannu ga Matasa"

Bikin zai gudana ne, Kamar haka;

Wuri: Jb Sakateriya, Gusau
Rana: 15-4-2018
Lokaci: 10:00

Sanarwa: Mashkur A Alkali Tsafe (Member a kwamitin Watsa Labarai na wannan bikin.)

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’