Oyo: An Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Fyade
Gangamin adawa da aikata fyade
Gwamnatin jihar Oyo ta yi gargadi tare da shan alwashin hukunta duk wani mutum da aka kama da laifin yin fyade a jihar.
Da yake tabbatar da wannan gargadi mataimakin gwamnan jihar Oyo, Moses Alake Adeyemo, yayi gargadin cewa duk wani mutum da aka kama da laifin yin fyade komai girman mukaminsa a kai rahotansa ga ‘yan sanda, don tabbatar da ganin doka ta yi aikinta.
Haka kuma mataimakin gwamnan ya bukaci mata a jihar da su rinka saka mai kyau don kaucewa jan hankalin masu yin fyade.
Hukuncin duk wani da aka kama da laifin yin fyade a jihar Oyo shine ‘daurin shekaru 14 a gidan kaso, shi kuma wanda aka kama da laifin lalata kananan yara zai fuskanci ‘daurin rai da rai.
A baya dai hukumar kididdiga ta kasa ta nuna cewa babban birnin tarayya Abuja da Legas sune aka fi samun rahotannin fyade masu yawa a Najeriya inda suke da alkaluma 58,566 kuma a jihar Legas aka fi samun fyade a shekarar 2016. A yayin da jihohin Katsina da Abia ke da karancin fyade a kasar.
Da yake ‘daukar matakin shawo kan matsalar gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayar da sanarwar daurin shekaru 35 ga duk wanda aka samu da laifin yin fyade.
Nura Muhammad Mai Apple Gusau
Comments
Post a Comment