BABBAN TARON KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA KASA RESHEN JIHAR ZAMFARA KARO NA UKKU YA 'KAYATAR!
Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau
Kasancewar kungiyar muryar talaka ta Kasa reshen jihar Zamfara kusan itace uwa mabada mama ga takwarorinta na wasu jihohin kasar nan, jiya Lahadi 15/04/2018 Tayi babban taronta Wanda ta Saba Duk shekara Wanda Wannan Karon shine karo na ukku, a cikin jerin kwanon shiraruwanta Wanda ta Saba Yi, Hakika Wannan Karon kusan zamu iya cewa ya samu Gagarumin nasara.
Irin yadda mun kaga shirin ya samu tsari mai kyau, ta hanyar yadda Anka rarraba membobin kungiyar kowane da nashi aiki, mutane da dama sun sauki darasi a cikin bayanan manyan Malamai, kamarsu Dr, Murtala Kaura, da Prof, Jibiya, ko shakka babu irin yadda sunka gabatar da bayanai wajan Abin sai dai Sam Barka.
Hakika 'YA'yan kungiyar muryar talaka reshen jihar Zamfara sun Nuna dattako matuka ainun, irin yadda sunka bada hadin Kai, ankayi Wannan babban Taron lafiya kuma munka kammala lafiya, Duk da wasu daga ciki, sunsu su bata tsarin ta hanyar yin kutse GA ayukan da ba'a sasuba. Amma Duk da haka muna godiya GA Allah da yanuna mana An kammala ba tare da wata Matsala ba.
Duk da irin aikin da anka bamu munso mu fuskanci turjiya ga jami'an tsaro, lokacin da munka so dauko wani hoto mai matukar muhimmanci amma kuma sunka hanamu, Kasancewar cincirindon jerin kwanon 'yan jaridu da 'yan Social media,
Mutane da dama sun amfana da Wannan Gagarumin shirin Musamman matasa wadanda sunka samu tallafin kayan sana'o'in hannu, da fatan Allah yasa zasuyi amfani da abinda sunka samu wajan ci gaban Kansu har su tallafawa wadan su, suma suci gajiyar abin.
Muna Addu'ar Allah ya taimaki kungiyar muryar talaka ta Kasa reshen jihar Zamfara da 'YA'yan kungiyar kwata,
Daga; Nura Muhammad Mai Apple Gusau
Comments
Post a Comment